Kano na yin nasara wajen darkake Korona a jihar – Ganduje

0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya shaida cewa tabbas jihar Kano na samun nasara a kokarin darkake Korona a jihar.

Sakataren Yada Labaran Gwamnan Kano, Awwal Anwar ya sanar da haka a madadin Gwamna Ganduje a Kano.

Gwamna Ganduje ya ce gwamnatin jihar ta maida hankali wajen tsananta yi wa mutane gwajin cutar a jihar ne a wuraren gwaji biyar da gwamnati ta kafa a fadin jihar.

Hakan ya sa mun iya yi wa mutane da dama gwajin cutar fiye da yawan wadanda Hukumar NCDC ta ce mu yi a duk rana wato mutum 100.

“Duk da yawan wuraren gwajin cutar da ake da su jihar Kano mukan aika da wasu samfurin da aka dauka daga nan Kano zuwa Abuja domin a yi musu gwajin cutar.

Anyi wa mutum 13,727 gwajin cutar, an samu mutum 1,262 da suka kamu, an sallami mutum 1003, mutum 52 sun mutu.

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 626 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Alhamis.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum -193, FCT 85, Oyo 41, Edo 38, Kwara 34, Abia 31, Ogun 29, Ondo 28, Rivers 26, Osun 21, Akwa Ibom 18, Delta 18, Enugu 15, Kaduna 13, Filato 11, Barno 8, Bauchi 7, Adamawa 5, Gombe 4, Sokoto 1.

Yanzu mutum 27,110 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 10,801 sun warke, 616 sun rasu.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum, 10,823, daga nan sai FCT – 2,020, Oyo – 1,432, Kano – 1,257, Rivers – 1, 114 , Edo – 1,203, Delta –1,149, Ogun –898, Kaduna – 818, Katsina – 578, Bauchi – 512, Gombe – 511, Borno – 501, Ebonyi – 438, Filato – 383, Jigawa – 318, Imo – 352, Abia – 351, Enugu – 342, Ondo – 353, Kwara – 269, Nasarawa – 213, Bayelsa – 234, Sokoto – 152, Osun – 148, Akwa Ibom – 104, Adamawa – 89, Niger – 116, Kebbi – 81 , Zamfara – 76, Anambra – 73, Yobe – 61, Benue – 65, Ekiti – 43, Taraba- 19 da Kogi – 4.

Share.

game da Author