Kadan Daga Dabi’u Da Halayen Sarki Muhammadu Sanusi II, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Dukkanin yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin mu Muhammad (SAW), da iyalansa da sahabbansa baki dayansu.

Ya ku al’ummah, wallahi a duk lokacin da nike magana akan Sarki Muhammadu Sanusi II, to lallai ku sani ina magana ne akan manyan halayensa masu kyau da dabi’unsa wadanda duniyar tarihi ta shaida, tun zamanin baya da zamanin da muke ciki yanzu. Dabi’u ne da halaye nagari, wadanda da ace duniya za ta rikesu, tayi koyi da su, to lallai da duniya ta zauna lafiya, a samu alheri da ci gaba. Wadannan dabi’u da halaye nasa kuwa, shi kan sa ya same su ne sanadiyyar koyin sa da fiyayyen halitta, wato Manzon tsira, Annabi Muhammad (SAW). Daga cikin dabi’u da halayen Sarki Muhammadu Sanusi II, akwai cewa:

Sarki Muhammadu Sanusi II, mutum ne mai hankali, mai hakuri da yafiya, kuma yana mai neman sakamakon haka a wurin Allah Subhanahu wa Ta’ala. Shi mutum ne mai yin abu domin Allah (wato da ikhlasi), mai kyakkyawar mu’amala ne ga mutane da kuma iyalan gidan sa. Mutum ne mai son gyara a koda yaushe, mutum ne shi mai umurni da aikata kyakkyawan aiki da kuma hani akan aikata mummunan aiki. Sarki Sanusi mutum ne mai son tsarki, mai tsafta, sannan shi mutum ne mai yawan kiyaye harshensa daga surutu da maganganun banza marasa amfani, sai fa idan a wurin fadar gaskiya ne. Sarki Muhammadu Sanusi mutum ne mai yawan ibada, mutum ne mai tausayi da saukin kai, mutum ne da Allah yayi masa kyawon sura da kyawon halitta, mutum ne mai tsantseni a rayuwar duniya, mutum ne da baya hana abun da aka tambayeshi, sai fa idan baya da shi, mutum ne mai karfin imani da tawakkali, mutum ne mai tausayi da son yara, mutum ne mai yin rangwame ga mutane, sannan shi mutum ne mai tsoron Allah da kamewa.

Imam Murtada Gusau

Imam Murtada Gusau

Ya ku jama’ah, wallahi Sarki Muhammadu Sanusi II mutum ne mai ciyar da abinci ga mabukata, mutum ne mai son taimako, mutum ne mai fadin gaskiya komai dacinta, kuma ko meye zai same shi akan hakan. Shi mutum ne mai kokari wurin girmama iyakokin Allah, mutum ne mai sakin fuska ga mutane, mutum ne mai rikon amana da cika alkawari, mutum ne jarumi, mai jarumta da rashin tsoro ko kokwanto, mutum ne mai karamci da jurewa akan haka, kuma shi mutum ne mai kunya.

Ya ku bayin Allah, Sarki Muhammadu Sanusi II mutum ne mai kankan da kai, mai tawadu’u, kuma shi mutum ne mai nuna rahama, tausayi da jin kai ga talakawa, kuma mutum ne mai saukin kai. Sarki mutum ne mai yafiya da hakuri kuma adali, mutum ne mai tsananin tsoron Allah, kuma shi mutum ne mai wadatar zuci da hakuri da kadan.

Daga cikin dabi’un Sarki Muhammadu Sanusi II, ya kasance shi mai son yin alheri ne ga kowa, kai hatta makiyansa. Sannan sai kusancinsa da fadawansa da talakawansa da kuma cudanya da su, da sauraren koke-koken su. Sannan sai kokarinsa wurin zuwa gai da marasa lafiya, ya biya kudin maganinsu, kuma yayi masu alheri, musulmi ne su ko kuma wadanda ba musulmi ba. Sannan sai rashin girman kan sa, da yin godiya ga duk wanda ya aikata masa alheri, da kuma kokarin saka masa shi ma, da abunda zai iya. Shi mutum ne mai son dukkanin wani abu mai kyau da tsabta da kuma kamshi, wato turare. Shi mutum ne mai son shiga tsakani da kuma kokarin yin sulhu a cikin dukkanin ayyukan alheri. Shi Mutum ne mai kokari wurin yiwa kansa hidima.

Jama’ah, wadannan kadan ke nan daga cikin halaye da dabi’un Sarki Muhammadu Sanusi II, wadanda duk wanda yayi hulda da shi, ko yake hulda da shi, to zai shaida hakan. Kuma kamar yadda nayi bayani, wallahi wadannan dabi’u da halaye, Allah ne yayi shi haka, ba shine yayi wa kan sa su ba. Sannan kuma ya same su ne sakamakon kokarinsa wurin bin umurnin Allah, na yin koyi da fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW). Sakamakon haka, a lokacin da yake kan gadon sarautar Kano, Kanawa da arewa suka ji dadi, suka yi murna da farin ciki. Aka wayi gari yana son su, suna son sa, kuma suna jin maganarsa, domin sun san ba zai yaudare su ba, kuma ba zai yi masu karya ba, kuma ba zai taba yarda a hada kai da shi a cuce su ba!

Ya ku jama’ah, wallahi wadannan kadan ke nan daga cikin hujjojinmu da dalilanmu na nuna kaunar mu da soyayyarmu ga wannan bawan Allah, da kuma kokarin kare mutuncinsa da martabarsa daga makircin makaryata, masu son bata masa suna. Jama’ah, bamu kadai ba ma, ni nayi imani da Allah cewa, duk wani mahaluki a duniya, duk wani mai gaskiya, duk wani mai son ci gaban al’ummarsa, mai ilimi da hangen nesa, wallahi dole yaso Sarki Muhammadu Sanusi II, ba don komai ba, sai don wadannan halaye da dabi’u nasa kyawawa, da Allah Subhanahu wa Ta’ala ya azurta shi da su. Ina rokon Allah yasa mu dace, amin.

Amma yau an wayi gari, tun da aka dau alhakinsa, babu wanda duniya zata kalla a Kano, wanda za ayi domin sa kuma a bari domin sa.

Kamar yadda kuka sani ne, a koda yaushe al’ummah ta kan tafi ne bisa jagorancin mutum daya, wanda ya kasaita, kuma yake da jajircewa da kokari akan abinda ya shafi jama’arsa da talakawansa, kuma yake son ci gabansu, sanadiyyar haka sai a samu zaman lafiya, kwanciyar hankali, da ci gaba mai dorewa da izinin Allah.

Amma babban abin taikaici, tun da Khalifah Mai Martaba Sarki Malam Muhammadu Sanusi II ya bar kujerarsa birnin Kano yake nema ya zama baya a idon duniya, an rasa ina aka dosa a birnin, kowa yayi tsit, komai yayi shiru, talakawa sun rasa gata. Komai ya lalace, ba ga sarauta ba, ba ga gwamnati ba, komai ya daina dadi, kuma baka bukatar ace ma da Sarki a Kano ko babu, duk dan Kano wallahi, yasan halin da birnin yake ciki, sai fa idan za mu munafunci kawunan mu ne, mu boye gaskiya, wannan kuma wani abu ne daban!

Ya ku jama’ah, abin alfahari ne ga dukkan dan Kano, ace a majalisar dinkin duniya, Sarki Sanusi yana da kujera tasa ta kansa, wadda duk taro na duniya idan ya tashi, za’a gayyace shi, kuma a gayyaci shugaban kasa, wanan ya ishi duk dan Kano alfahari.

Sarki Muhammadu Sanusi II, a yau duniya kalar sa take nema, kuma take bukata, domin shi din, dole sai da ire-iren su, kuma wannan matsayin daga Allah ya same shi, ba wai yin kan sa bane, a’a.

A dalilin sa ya sake daukaka darajar Kano a idon duniya, amma yanzu Kano sai kokarin komawa baya take yi, saboda an kawo wani iri, wanda an rasa ma ina ya dosa, babu Sarauta, babu karatun, bare ace Kano za ta ci gaba. Allah ya sawwake, amin.

Wannan bawan Allah, Sarki Muhammadu Sanusi II, ya sanya Kano ta zama abin alfahari a idon duniya, kuma babu kamar sa har yanzu.

Muna rokon Allah ya saka masa da alkairi, kuma ya ci gaba da kare shi, ya kare masa mutuncinsa da martabarsa, daga sharrin miyagu, mahassada, magauta da makiya, amin.

Ya Sarki Sanusi, wallahi kai ne Sarki a wurin talakawa, ko yau ko gobe, ko jibi, ko anjima, ko yanzu Kanawa basu da kamar ka.

Ya Allah mun tuba, ka yafe laifukan da muka yi maka, ka dawo muna da Sarkin mu, mai son ci gaban jihar Kano da arewa da Najeriya, kuma mai kaunar talakawa, amin.

Ina rokon Allah ya kyauta, ya kawo muna mafita ta alkhairi, amin.

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author