Rundunar Sojin Najeriya ta bayyan cewa mahara da ‘yan bindiga da dama na mika wuya a jihohin Zamfara da Katsina a sanadiyyar balbalin wuta da suka sha daga dakarun sojojin Najeriya.
Kodinatan yada labaran rundunar Sojin, John Enenche ya bayyana cewa zaratan dakarun soji sun afkawa maboyar ‘yan bindiga a dazukan da ke kewaye da jihohin Katsina da Zamfara inda suka rika dirawwa maboyar mahara suna dagargaza su.
Ya kara da cewa baya ga dagargaza maharan wasu da dama sun mika wuya sannan sun bada makaman su.
Enenche ya yi kira ga maharan da su mika wuya ko kuma su sha azabar luguden balbalin wutan sojojin rudunar “Operation Hadarin daji”.
Idan ba a manta ba, gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya shaida cewa baya tantama ko haufin zaman sulhu da yayi da shugabannin ‘yan ta’adda da mahara dake jihar domin samun maslaha a jihar.
Matawalle ya ce wannan zama da suka yi da ‘yan ta’adda ya haifar wa jihar da Alkhairi domin da yawa sun mika wuya.
” Nasarorin da muka samu a cikin wata shida shine gwamnatin baya ta kasa samu cikin shekara 8 da ta yi tana mulkin jihar. Muna farin ciki ga nasarorin da muka samu kuma za mu ci gaba da tattaunawa da wadanda suka yi mana taurin kai.