Jihohin Yarabawa na duba yiwuwar bude makarantu domin dalibansu su rubuta jarabawar WASSCE

0

Daukacin Jihohi shida na yankin Kudu maso Yamma, sun fara tunanin sake bude makarantun sakandaren jihohin, domin bada damar daliban shekarar karshe su zauna jarabawar fita sakandare, wato ‘West African Senior Secondary Certificate Examination’, da aka fi sani da WASSCE.

Jihohin da ake kira jihohin Yarabawa, sun kunshi Ekiti, Lagos, Ondo, Oyo, Osun da kuma Ogun.

Sun yanke wannan shawara ce a wani taron da Hukumar Kare Muradin Jihohin Kudu Maso Yamma (DAWN) ta shirya tare da kwamishinonin ilmin jihohin da mashawartan gwamnoni a bangare ilmi na jihohin shida.

Taron kuma ya hada har da Shugabannin Hukumar Kula Da Ilmi na jihohin shida.

Wannan mataki da suka dauka, ya fito ne mako daya bayan Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa dalibai ba za su yi zaman rubuta jarabawar WASSCE ta 2020 ba, saboda barkewar cutar Coronavirus.

Ko a ranar Laraba sai da gwamnatin tarayya ta kara nanata wannan matsaya da ta dauka.

Sai dai kuma cikin wani rahoto wanda Babban-Daraktan Hukumar DAWN, Seye Oyeleye ya sa wa hannu, ya ce kwamishinonin jihohin Ekiti, Ondo, Oyo, Osun, Ogun da Lagos, duk sun nuna cewa a shirye suke da a bude makarantun sakandare, domin dalibai su samu damar rubuta jarabawa.

Sai dai kuma sun roki Gwamnatin Tarayya ta sa a dage fara jarabawar, a kara makonni uku.

Ya ce wannan abu ne dogara ne rokon da WASSCE za ta yi wa Hukumar Jarabawar GCE da a shirya farawa ranar 24 Ga Agusta.

Taron na su ya kuma amince cewa idan dai har sun hakkake za su bude makarantun, to za su ba kayan aiki da ma’aikatan da za su rika kula da daliban da kuma shatawa da gindaya ka’idoji a makarantun da kuma cikin ajujuwa.

Sannan kuma za su zuba jami’an kula da lafiya wadatattu a makarantun.

A bangaren jarabawa kuma, sun shawsrci Hukumar Shirya Jarabawa ta bi tsarin rubuta jarabawa da kwamfuta.

Sai dai kuma a ranar Larabar da DAWN ta gudanar da wanann taron, ita ma Gwamnatin Tarayya a ranar ta sake nanata cewa ta na nan a matsayin da ta dauka cewa ba za a zauna jarabawar WASSCE a 2020 ba.

Sai dai kuma gwamnati ta hannun Karamin Ministan Ilmi, ta ce ta na ci gaba da tattauna batun da dukkan bangarorin da batun ya shafa, domin a cimma matsaya guda.

Share.

game da Author