Kwamishinan ilimi na jihar Neja Hannatu Salihu ta bayyana cewa gwamnati ta ware naira miliyan 86 domin ciyarwa da daukar dawainiyar almajirai daga jihar zuwa jihohin su.
Hannatu ta fadi haka ne wa manema labarai ranar Alhamis a garin Minna.
Kwamishina Hannatu ta ce gwamnati ta yi haka ne domin yin biyayya ga matsayar da kungiyar gwamnonin Najeriya ta yi na maida dukka almajirai zuwa jihohinsu na asali.
” Gwamnati ta amshi almajirai 86 da aka dawo da su daga wasu jihohi sannan ta maida su ga iyayensu.
Gwamnati ta maida almajirai 557 garuruwan su daga jihar Neja, sannan hukumar kare hakkin Yara ta jihar ta mai da wasu almajirai 139 ga iyayensu.
Daga ciki 12 baki ne daga wasu kasashe sannan biyu sun manta garin da su ta asali.
Daga nan sai ta ce gwamnati na tsara wasu matakai domin ganin ba a samu matsala ba idan aka dawo makarantun gwamnati na samar wa yara kariya daga kamuwa da korona.
Mutum 26,484 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 10,152 sun warke, 603 sun rasu.
Mutum 116 ne suka kamu da cutar a jihar Neja, 64 na kwance a asibitocin killace masu fama da cutar,45 sun warke sannan 7 sun mutu.