Jibga-jibgan harkalla 9 da Magu ya taf a hukumar EFCC – Binciken Kwamitin Shugaban Kasa

0

Wani abin tashin hakali da mamaki shi ne yadda dakataccen shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya kasa fadin inda wasu kadadarori na rukunin gidaje sama da 332 cikin 836 da hukumar EFCC ta kwato a 2018, kamar yadda kwamitin bincike ya bayyana.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ta ruwaito, bisa ga bayanan da kwamitin ya mika mata, kwamitin ya gano yadda aka barnatar da wasu kaya da ya hada da motoci, Jiragen ruwa da gidaje da aka bar su suka lalace saboda rashin kula.

An gano wasu kadarorin da aka banzartar dasu suka lalace shekaru 15 da kwato su.

” Akwai wasu jiragen ruwa dake dakon danyen mai da aka kyale su suka bace bat batare da an kula da su ba wanda suna karkashen kulawar hukumar EFCC din ne.

kuma kwamitin shugaban kasa ya gano cewa ‘yan kwangilan da hukumar EFCC ta yo hayar su duk basu iya kula da dimbin dukiyar da hukumar ta kwato a hannun barayin gwamnati ba.

Magu ya karya dokar saida kadarorin da hukumar ta kwato, domin an gano ya saida wasu kadarorin ba tare da ya yabi doka ba. Sannan kuma an gano cewa kwata-kwata babu wani tsari da hukumar ta yi karkashin Magu kan yadda za ta rika sani da yadda ake gudanar da ayyukan rassan hukumar dake jihohi, komai ya tabarbare a hukumar.

Kwamitin ya gano cewa wasu daga cikin manyan darektocin hukumar sun waske da kadarorin da aka kwato sun cin karen ba babbaka kawai abin su.

Sannan kuma An gano cewa Magu na saida wa ‘yan uwa da abokan arziki kadarorin da aka kwato kudi kalilan don son rai.

An gano cewa yana da asusun ajiyar kudi a bankuna da dama da amfani da wasu boyayyun sunaye da suke rika loda masa rabon sa a wasu asusun ajiya na boye.

Share.

game da Author