JARABAWAR SAKANDARE: Najeriya za ta yi amfani da sakamakon GCE madadin WASSCE a 2020 – Minista

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa mai yiwuwa ta ce dalibai su rubuta jarabawar GCE a cikin watan Nuwamba, matsawar aka kasa kammala shirye-shiryen rubuta jarabawar WASSCE, ta Afrika ta Yamma cikin lokacin da aka tsaida.

GCE jarabawa ce ta daban, wadda ake rubutawa cikin watan Nuwamba kuma a fito da sakamakon ta cikin watan Disamba.

Karamin Ministan Harkokin Ilmi, Emeka Nwajuiba ne ya bayyana haka a taron manema labarai na mako bib-biyu a kan halin da ake ciki dangane da cutar Coronavirus a kasar nan.

Minista ya ce wannan canji ya zama tilas ganin cewa babu wani dalilin da zai sa a kara wa’adin lokacin rubuta jarabawar WASSCE.

PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda gwamnatin tarayya ta bayyana fasa komawar dalibai makarantu, bayan da ta rigaya ta aza ranar komawa.

Sannan ta ce babu wata makarantar sakandare a Najeriya da za ta bude har dalibai su rubuta jarabawar WASSCE tsakanin 5 Ga Augusta zuwa 5 Ga Satumba.

An cimma wannan matsaya ce domin kauce wa yiwuwar kamuwa da cutar Coronavirus ga dakibai saboda cunkoso a dakunan rubuta jarabawa.

Sannan kuma Najeriya, Ghana, Sierra Leone, da Gambia su na kokarin shawo kan lamarin yiwuwar dage ranar fara jarabawar.

Minista ya ce ci gaba da fantsamar cutar Coronavirus bagatatan ya sa har yanzu jihohi ba su shirya komawar dalibai makarantu ba.

Share.

game da Author