Jami’an NSCDC ta damke gogarman ‘yan ta’adda da ya addabi mutan Adamawa

0

Hukumar tsaro na ‘Sibul Difens’ NSCDC na jihar Adamawa ta Kama gogarman ‘yan ta’adda Michael Linus, da ake Kira Damudu.

Shugaban hukumar Nuradeen Abdullahi ya Sanar da haka ranar Talata da yake gabatar da ‘yan ta’addan da Jami’an tsaro suka Kama a jihar ga manema labarai a garin Yola.

” Ba tun yanzu ba muke farautar wannan kasurgumin dan ta’adda. Baya ga aikata dabanci da yake yi a unguwanni, Damudu na saida wa kananan yara da manyan muggan kwayoyi da kuma lalata yara ta hanyar dulmiya su cikin wannan mummunar hanya.

” Jami’an mu kuma su damke wasu gaggan fitsararrru da suka addabi mutane Suma a jihar, daya sunan sa Ibrahim Mohammed, mai shekara 33 wanda Dan damfara ne da wani Mustapha Ismail da ya shahara wajen satar motoci.

Sannan kuma jami’an sun kama wasu matasa da da suka shahara wajen damfarar mutane ta yanar gizo, wato ‘yan yahoo-yahoo.

A karshe hukumar tsaro na Sibul Difens din ta shaida cewa za a gurfanar da wadannan ‘yan ta’adda a kotu sannan kuma za a ci gaba farautar irin wadannan Yan ta’adda da yara domin kawo karshen ta’addanci a jihar.

Share.

game da Author