Illar Karatun Boko Babu Koyan Sana’a, Daga Mukhtar Umar Lere

0

Ci da Boko zalla yau a Najeriya ya zama gaggarumin ci da hakkin Al-Ummah. Domin ƴan Boko ne suka wawure arzikin Najeriya kuma har yanzu su ke wawurewa.

Duk wani muƙami da ka sani a gwamnatance da kampanoni ƴan Boko ne ke riƙe da su a yau. Wanda ya yi karatu a tsangaya ko a zaure zalla, sai dai ya yi aikin masinja ko gadi indai a ma’aikata ne.

Kowa ya san kashe 95 na ƴan Boko ‘ƴan jiran albashi ne, kuma ko wanda albashinsa ba zai iya riƙe shi ba idan bai wawura ba. Ke nan irin karatun Bokon da mu ke yi zalla babu koyon sana’a sannan babu fahimtar Addini baya koya wa Al-Ummarmu komai sai girman kai da ha’inci. Ci da halal ya yi mutuƙar ƙaranci a ƴan Boko yau.

Jiji da kai a cikin ƴaƴan Sarakai ne ake samu, musamman wanda ya haɗu da wayewan karatun Boko, hakan kuma lallai abin zargi ne a wajen Allah da bayinSa Salihai, amma matsalar ita ce ɗan talaka ya koya har yafi iyawa.

Za kaga mutum gidansu sun gaji jima, ƙira ko wanzanci, amma saboda ya yi karatun Boko, yanzu yafi ƙarfin ya yi wannan sana’ar, idan aka alaƙanta shi da wannan sana’ar sai yaji an ci masa fuska. Ya kasa gane karatun Bokon da ya yi zai taimake shi wajen bunƙasa sana’ar gidansu ya ci abinci har ya ɗauki mutane da yawa aiki kuma ya koya ma mutane da yawa aiki.

Kayan da ake shigowa da su daga ƙasashen duniya na bukatun yau da kullum da su ke burge shi masu sana’a irin na gidansu ne suka ƙera su ta hanyar zamunantar da su.

Wallahi lokaci na nan zuwa idan ɗan Boko bai iya sana’a ba, ba zai ci abinci ba. Muna ganin yadda ‘ƴan boko suka dage sai aikin ofis kuma babu guraben aikin, wanda su ke cikin aikin kullum rage su ake yi, musamman a wannan jihar.

Dole sai mun chanza salon rayuwa. Allah Ya taimake mu wajen gano matsalolinmu mu gyara tun kafin mu bar duniya, ameen.

Mukhtar Umar Lere, Magajin Mallam Wunti

Share.

game da Author