Hukumar NSTIF ta amince ta kashe naira bilyan 3.4, ‘amma da amincewar Minista Ngige’

0

Dakatattun shugabannin Hukumar NSITF, sun bayyana cewa tabbas an kashe naira bilyan 3.4 da ake ta sa-toka-sa-,katsi a kan su.

Sai dai kuma sun yi ikirarin cewa dukkan ayyukan da aka gudanar da kudaden, an yi ne da sa hannun amincewar shi Ministan Harkokin Kwadago, Chris Ngige.

Cikin wata sanarwa da suka fitar a matsayin raddi, sun ce ba gaskiya ba ne da ofishin minista ta hannun kakakin yada labaran sa da ya ce an ksrkasa kwangiloli har gida 196.

Sun ce kudaden an kashe su ne a cikin shekarar 2017, 2018 da kuma 2019 wajen bayar da horo ga ilahirin ma’aikatan hukumar na kasa baki daya, su 5000 a cikin wadancan shekaru da aka lissafa a sama.

Sun ce babu wani batun bayar da kwangilolin gina ofisoshin shiyya 14 a fadin kasar nan, ba tare da amincewar Hukumar Gudanarwar NSITF ba.

Sun kuma yi zargin cewa bayan dakatar da su, an kwashe kwafe kwafen takardun bayanai masu nuna gaskiyar su day kuma hujjar Minista Ngige din ne ya bayar amincewa da umarnin kashe kudaden.

Sai dai kuma Minsta ya umarci da su gabatar da hujjojin su ga kwamitin bincike kawai idan har su na da hujjojin.

A gefe daya kuma, Kungiyar Kwadago reshen NECA, ta yi korafin cewa Ngige ya yi gaggawar dakatar da wadanda aka dakatar din.

Sun ce Ngige yayi gaggawa ba tare da jiran shawara daga Shugabannin Hukumar Gudanarwar NSITF ba.

Shi dai Ngige ya jajirce cewa ba shi ya dakatar da su ba, umarni ne daga Ofishin Shugaba Muhammadu Buhari.

Share.

game da Author