Hukumar NDDC ta ci amanar al’ummar Neja-Delta – Gbajabiamila

0

Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ya yi kakkausan korafin cewa duk da dimbin bilyoyin nairori da gwamnatin tarayya ke narkawa cikin asusun Hukumar Bunkasa Yankin Neja-Delta, har yau
hukumar ba ta aiwatar da wani aikin kirki da za a jinjina mata ba.

Gbajabiamila ya yi wannan jawabi a wurin zaman Kwamitin Majalisa Mai Binciken Badakalar Kudaden da aka kashe a wata mummunar harkallar bilyoyin kudaden da ake ci gaba da fallasawa.an tafka a NDDC din.

Shugaba Muhammadu Buhari ne a cikin 2019 ya bada umarnin a yi binciken filla-filla na yadda aka narkar da kudaden NDDC, tun daga 2001 har zuwa 2019.

NDDC hukuma ce da gwamntin tarayya ta dora wa alhakin bunkasa jihohin yankin Neja-Delta mai dimbin arzikin man ferur.

Jihohin sun hada da Bayelsa, Rivers, Cross River, Edo da Ebonyi.

Daga cikin alhakin da aka dora wa hukumar akwai ilmantar da matasan yankin, ba su horo da samar musu ayyukan dogaro domin su watsar da tashe-tashen hankulan da suka hada da fasa bututun mai da kai wa masana’antun haki danyen mai hare-hare.

Gbajabiamila ya ce a shekaru 20 da NNDC ta shafe aka narkar mata makudan kudade, al’ummar yankin ba su amfana da wani abin kirkin da za a iya tutiyar cewa NDDC ts tsinana musu ba.

“Saboda haka abin takaici kuma abin kunya ne a ce bayan biiyoyin kudaden da ake narka wa NDDC, babu wasu labarai na abin arziki dagsa yanzu sai labaran fallasa harkallar wawura da satar makudan kudade.

Ya ce makasudin binciken don a gano hanyar da kudaden hukumar ke zurarewa da kuma gano wadanda suka kwashe kudadden, domin dinke bakin aljihun da suke sace kudaden.” Inji Gbajabiamila.

Share.

game da Author