Hukumar Kula da Ma’aikatan Majalisar Dattawa da ta Tarayya (National Assembly Service Commission), ta nada sabon Shugaban magatakardar majalisar Kasa bayan sauke wanda ke kai, Mohammed Sani-Omolori.
Sabon Akawun shine Olatunde Ojo, an ba shi riko ne. Ya fito daga garin Ilobu, Hedikwatar Karamar Hukumar Irepodun daga jihar Osun.
Hukumar ta kuma sanar da sabbin masu rike da mukamai, ciki har da Mataimakin Shugaba na Majalisa, Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Majalisar Dattawa da na Tarayya, Sakatarori da Daraktoci da sauran mukamai da dama.
Shugaban Hukumar NASC, Ahmed Amshi ne ya bayyana sunayen sabbin nade-naden, cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, mai dauke da sa hannun Amshi din da kan sa.
Hakan ya faru ne bayan hukumar ta yi wani taron gaggawa, a ranar Juma’a, 19 Ga Yuli.
Sanarwar ta ce Mohammed Bala ne sabon Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Majalisar Gaba-daya, wato mataimakin sabon da aka nada. Shi kuma El-Ladan Dauda Mataimakin na Majalisar Dattawa, yayin da shi kuma Patrick Giwa zai ci gaba da rike mukamin sa na Shugaban Ma’aikatan Majalisar Tarayya, har zuwa lokacin ritayar sa, a karshen Nowamba, 2020.
An nada Yusuf Dambatta sabon Sakataren Hukumar Kula da Ma’aikatan Majalisa.
Tirka-tirka
Wannan hukuma ta nada hannun dambe da Sani-Omolori da wasu ma’aikatan Majalisar su 160, wadanda lokacin ritayar su ya yi, amma su ka ki sauka yin ritaya a bisa hujjar su cewa Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dattawada ta Tarayya sun kara yawan shekarun yin ritaya.
Bisa ka’ida dai sai mutum ya cika shekaru 60 da haihuwa, ko kuma ya shafe shekaru 35 ya na aiki sannan ritaya ta wajaba a kan sa.
A ranar Laraba ne dai Amshi ya sanar da manyan ma’aikatan Majalisar cewa duk wanda ya cika shekaru 60 ko kuma ya kai shekaru 35 ya na cikin aiki, to ya gaggauta yin ritaya.
Sani Omolori dai ya cika shekaru 60 a duniya, amma kuma ya ce ba zai sauka ba shi da sauran manyan ma’aikatan 160, saboda Majalisa ta yi wa Dokar Ritaya kwaskwarima daga shekaru 60 aka maida shekaru 65.
Sai kuma tsawon shekarun aiki daga 35 zuwa 40. Kuma suka ce dokar ta fara aiki daga 2019.
Sai dai kuma duk da wannan, sai Hukumar NASC a karkashin Ahmed Amshi ta yi kunnen-uwar,-shegu da wadannan dalilai, ta bayar da sanarwar sabbin d ta ce ta nada.
Sai dai Omolori ya ce doka ba ta da iznin sauke shi a yanzu, saboda an yi mata kwaskwarimar cewa sai nan da karin shekaru 5 a matsayin sa na ‘Clerk’ din Majalisa zai yi ritaya.