Kotu a Nyanya, Abuja, ta tsare wani magidanci mai suna Abdul Abdulkadir a dalilin dirka wa matan makwabcin sa rushehen dutse a cikin ta da yayi sanadiyyar barin cikin wata hudu da take dauke da shi.
‘Yan sanda sun kama Abdulkadir bisa laifin kashe jaririn da ba a haifa ba.
Lauyan da ya shigar da karar, Okokon Udo ya bayyana cewa, Abdulkadir da makwabcin sa Adebayo na haya a wani gida dake Kabusa.
” Wata rana rigima ya barke a tsakanin su, daga nan sai suka kaure da dambe, zage-zage da naushe-naushe. Ana haka ne Abdulkadir ya rarumi dutse ya auna abokin fadan sa Adbayo ya aika masa da ita, abinka da rashin seti, maimakon dutsen ya dira kan Adebayo, sai ya dira cikin matarsa da ke gefe tana taya mijin ta a filin tsakar gidan su.
Nan take matar Adebayo ta fadi kasa sharaf sume. Daga nan kuma sai fada ya kara gaba daya aka dunguma sai asibiti. Bayan likitoci sun duba ta sai suka tabbatar wa mijin ta wato Adebayo cewa matar sa fa tayi barin wannan ciki.
Lauyan dake Kare Abdulkadir, Etta Effion ya nemi kotu ta bada belin Abdulkadir.
Alkalin kotun Peter Kekemeke ya bada belin Abdulkadir akan naira miliyan biyar tare da shaidu biyu.
Kekemeke ya ce daya daga cikin sharuddan belin sun hada da samo shaidan dake da mallakin fili a Abuja sannan ya gabatar da takardun shaidan filin a zaman da kotun za ta yi nan gaba.
Za a ci gaba da shari’an ranar 15 ga watan Oktoba.