HEPATITIS: Rashin Sani, kin yin gwaji na daga cikin dalilan da ya sa mutane ke fama da cutar a Najeriya

0

Ranar 28 ga Yulin kowace shekara ne ranar da kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta ware don wayar da Kan mutane game da cutar hepatitis a duniya.

Cutar ta yi tsanani a dalilin rashin sani, rashin yin gwajin cutar da tsadar magani da mutane ke fama da su.

Bincike ya nuna cewa duk shekara cutar na yi ajalin akalla mutum miliyan 1.4.

A Najeriya mutum miliyan 17 zuwa 20 na dauke da cutar ba tare da sun sani ba sannan da dama daga cikin mutane kan sani suna dauke da cutar ne a lokacin da tayi tsanani a jikin su da magani ba zai iya musu aiki ba.

Alamun kamuwa da cutar Hepatitis sun hada da canja kalar fatar jikin mutum zuwa kalar ruwan kwai, farin kwayar ido,amai, yawan jin gajiya a jiki,ciwon ciki, yawan zuwa bahaya da sauran su.

Taken taron na bana shine ‘Dakile yaduwar cutar hepatitis B musamman a jikin mata da jarirai sannan da wayar da Kan mutane yayin da duniya ke yaki da cutar covid-19’.

Hanyoyin hana yaduwar cutar

Wani likita mai suna Mike Omotosho ya yi kira ga mutane da su rika zuwa asibiti domin yin gwajin cutar musamman ganin cutar baya nuna alamu a jikin Mutum.

Ya ce yin haka zai taimaka wajen Hana cutar yin ajalin mutum sannan zai taimaka wajen hana yada cutar.

Bayan haka wata likita dake aiki a asibitin Asokoro Nnabuchi Chidinma ta yi kira ga gwamnati da ta taimaka wajen wayar da kan mutane game da cutar da hanyoyin samun kariya daga kamuwa da ita.

Abubuwa 9 game da Hepatitis B da C

1. Cutar hepatitis B da C cututtuka ne dake kisan miliyoyin mutane a duniya duk shekara.

2. Cutar kan zama cutar dajin dake kama huhu idan ba a gaggauta neman magani ba wanda hakan kan yi ajalin mutane miliyan 1.34 a duniya.

3. Hepatitis B da C na daga cikin cututtukan da basu nuna alamu idan an kamu da su sai dai dole an yi gwaji.

4. Wadannan cututtuka na da nasaba da kashi 60 bisa 100 na cutar dajin

5. Matsalolin rashin yin gwaji da kula na cikin matsalolin da ya kamata a kawar da su kafin nan da shekarar 2030.

6. Yin gwaji da wuri da shan magunguna ne mafita daga wadannan cututtuka.

7. Cutar na iya kashe mutum farat daya idan ba a shan magani.

8. Ana iya kubuta daga kamuwa da cutar ko kuma a warke idan an kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da cutar.

9. Ana iya kamuwa da cutar idan ana amfani da abin da mai dauke fa cutar yayi amfani da kamar su reza, abin aski da sauran su.

Abubuwa 7 game da maganin rigakafin cutar Hepatitis (Hepatitis B Vaccine)

1. An sarrafa maganin rigakafin cutar Hepatitis daga cutar Hepatitis wanda idan ya shiga jikin mutum yake kare shi daga kamuwa da cutar.

2. Wannan maganin na kare mutun daga kamuwa da Hepatitis B ne kawai.

3. Ana bada rigakafin maganin sau uku ko hudu a cikin watanni shida domin samun kariya daga kamuwa da cutar.

4. Za a iya yi wa jarirai allurar rigakafin wannan cutar.

5. A yi rigakafi.

Share.

game da Author