HARKALLAR NDDC: Kotu ta hana ‘yan sanda kama Nunieh

0

Babbar Kotun Jihar Rivers ta hana Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya kama Joi Nunieh. Sannan kuma ta hana su tsare ta ko ci gaba da yi mata duk wata barazana.

‘Yan sanda na farautar ta bisa zargin yi wa w.ani kage da kazafi.

Ranar Alhamis ce jami’an tsaro suka dira tun karfe 4 na asubahi, suka kewaye gidan ta a Fatakwal. Har kokarin kutsawa gidan suka so yi da karfin tsiya, kamar yadda wani bidiyo da aka watsa a soshiyal midiya ya nuno su.

Daga baya ne Gwamna Nyesom Wike na Rivers ya je tare da wasu jami’an gwamnatin sa, ya kubutar da ita zuwa Gidan Gwamnatin Jihar Rivers a birnin Fatakwal.

A ranar Juma’a sai Kwamishinan ‘Yan Sanda ya nemi Gwamna Wike ya damka musu Nunieh, saboda binciken ta da ya ce ake yi da zargin dankara wa wani kazafi.

A wannan ranar Nunieh ta garzaya kotu, inda Mai Shari’a E. N Thompson ya umarci ‘yan sanda kada su sake su kama ta.

Wadanda Nunieh ta maka kotu, sun hada da Ministan Neja-Delta, Godswill Akoabio, wanda ta zarga cewa ya yi kokarin yin lalata da ita, amma ya hakura bayan ta zabga masa mari.

Ta kuma hada da Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Rivers,. SSS da kuma Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya gaba daya.

Kotu kuma ta yi gargadin a gagguta janye ‘yan sandan da aka girke a kofar gidan Nunieh.

Daga nan aka dage karar zuwa 27 Ga Yuli, 2020.

Nunieh ta yi shugabancin riko na Hukumar Bunkasa Yankin Neja-Delta (NDDC) na tsawon watanni hudu.

Cire ta ya haifar da fallasa tsakanin ta da Ministan Neja-Delta, Akpabio da ta yi ikirarin shi ne kanwa uwar gamin cire ta, saboda ta ki yi masa rantsuwa a asirce ba za ta fallasa duk wata harkalla da ya tabka ba.

Sannan kuma ta ce ya nemi yin lalata da ita, amma ta ki amincewa, har ta kai ga ta wanka masa mari a fuska.

Share.

game da Author