HARIN KWANTAR BAUNA: ‘Yan bindiga sun kashe sojoji 16, sun raunata 28 a Katsina

0

Akalla Sojoji 16 ne suka rasa rayukansu a wani harin kwantar bauna da ‘yan bindiga suka yi wa sojojin Najeriya a Shimfida dake karamar hukumar Jibia, jihar Katsina.

Cikin sojojin da aka kashe akwai, Manjo daya, Kaftin daya, da Laftanal daya.

Majiyar mu ya shaida mana cewa maharan sun afkawa sojojin dake tafiya da kafa a cikin wannan daji Shimfida inda suka bude musu wuta daga saman tsaunuka dake kewaye da dajin.

Bayan haka sun ji wa wasu sojoji 28, rauni.

kakakin rundunar ‘yan sandan Sagir Musa ya ce ba shi da masaniyar haka kuma ba zai iya cewa komai akai ba.

Jihar Katsina na daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga. Bayaga jihar, Jihar Zamfara da Kaduna ma suna fama da ire-iren hare-haren ‘yan bindiga kamar haka.

A watan jiya, dayawa daga cikin mazauna kananan hukumomin jihar Katsina sun rika fitowa suna gudanar da zanga-zanga domin nuna bacin ransu game da kashe-kashe da garkuwa da mutane da yayi tsanani a jihar.

Hakan ya sa shugaba Muhammadu Buhari wanda dan asalin jihar ne ya umarci sojojin kasar nan su koma jihar domin kakkabe wadannan mutane cikin gaggawa.

Haka kuma a wani rahoto da da aka buga a jaridun kasar nan, an gano cewa shugaban Boko Haram Abubakar Shekau, na kakkafa sansanoni kara yawan mabiya a yankuna kasar nan.

Share.

game da Author