HARAJIN LA’ADA WAJE: Gwamnati za ta rika tatsar naira tiriliyan 1 a duk shekara daga jikin ‘yan Najeriya

0

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin karbar harajin-la’ada-waje, da aka fi sani da ‘stamp duty’ na tsabar naira tiriliyan 1 a duk shekara daga jikin ‘yan Najeriya.

Da ya ke jawabi wajen kaddamar da shirin a Abuja, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, wanda ya wakilci Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce an kaddamar da shirin ne domin ya zama hanya ta biyu ta samun kudin shiga ga gwamnatin tarayya baya ga danyen man fetur.

An dai kaddamar da Kwamitin Ministoci ne da za su aiwatar da wannan gagarimin shirin karbar kudade masu tarin yawa, amma kuma a hanya mai sauki, daga jikin ‘yan Najeriya.

Gwamnati ta ce ganin yadda harkar cinikayyyar danyen man fetur ta tabarbare a duniya, ya zama tilas a bijiro da hanyoyin samun kudin shiga a cikin gida.

Za mu tatsi tun na 2016 zuwa yau da ba mu tatsa a baya ba – Gwamnati

Da Mustapha ke jawabi a madadin Buhari, ya ce an umarci Hukumar Tattara Kudaden Shiga (FIRS), wadda aikin karbar harajin ke hannun ta, ta tabbatar ta karbo dukkan harajin ‘stamp duty’ tun daga 2016 zuwa yau da ba a karba a baya ba.

Daga nan sai aka umarci hukumomin gwamnatin tarayya (MDA’s), FIRS, NIPOST su bada kyakkyawan hadin kai domin samun nasarar shirin.

Mustapha ya sanar da cewa dukkan kudaden da za a tara, Hukumar FIRS za ta rika zuba su ne a cikin Asusun Gwamnatin Tarayya na cikin Babban Bankin Najeriya, CBN.

Bayan Shugaban Hukumar Tara Kudaden Haraji, Muhammed Nami ya yi karin haske, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan da Kakakin Majalisar Tarayya,, Femi Gbajabiamila, sun tabbatar da cewa Majalisa za ta bayar da hadin kai sosai domin tabbatar sa samun nasarar shirin.

Bambancin Harajin-La’ada-waje (Stamp Duty) Da Harajin-jiki-magayi (VAT):

1. Harajin-jiki-magayi kudi ne da Gwamnatin Tarayya ke tatsa har kashi 7.50% na kayan da kwastoma ya saya a kantina.

Ba kowane abin da aka saya ne ake tatsar karin kashi 7.5% ma adadin yawan kudin kayan da kwastoma ya saya ba. Akwai kayayyakin da aka tantance su ne ake biya wa harajin ‘VAT’.

Kudin na tafiya ne ga gwamnatin tarayya, ba aljihun kantin da kwastoma ya yi sayayya ba.

A baya kashi 5% bisa 100% ake biya, amma da Buhari ya sake nasara zango na biyu, sai gwamnatin sa ta kara kashi 50 bisa 100. Wato daga 5% zuwa 7.5.

2. Harajin-la’ada-waje (Stamp Duty)

Shi kuma haraji ne gwamnatin tarayya za ta rika tatsa daga jikin kwastoman da ya biya kudade ya zuwa asusun wani kamfani, masana’antu ko wani mutum da sunan harkokin ciniki.

Haka kuma duk wasu kudaden da kwastoma ko mai ajiyar kudi a banki ya ajiye ko ya aika a banki, muddin sun kai naira 10,000, to ko sau nawa ka zuba ko ka aika kudin a banki, sai an ciri naira 50 ta la’ada-waje.

Share.

game da Author