Har yanzu ba a samu bullar Korona a Jihar Koros Ribas – Gwamna Ayade

0

Gwamnan jihar Koros Ribas, Ben Ayade ya bayyana cewa jihar sa bata samu bullar Korona a ko ina a fadin jihar ba.

Ayade ya ce jihar sa na nan cikin tsarkin rashin Korona, wanda ita kadai ce jiha daya tal da cutar bata bulla a cikin ta ba a Najeriya.

Gwamnan ya jaddada haka ne da yake tattaunawa da kwamtin yaki da dakile yaduwar cutar na jihar ranar Alhamis, a babban birnin jihar, Kalaba.

Ayade ya yabawa kokarin da gwamnati ta yi wajen amfani da ‘Polymerase Chain Reaction (PCR)’ wajen yin gwajin cutar covid-19 a kasar nan.

“Yanzu da muka bude iyakokin jihar ya Zama dole mutane su Kara kiyeye sharuddan gujewa kamuwa da cutar.

Gwamnan ya mika godiyarsa ga ma’aikatar kiwon lafiya da hukumar NCDC Kan kokarin da suka yi wajen dalike yaduwar cutar.

Shugaban kwamitin yaki da cutar covid-19 na jihar Betta Edu ya shima ya yaba kokarin da Kwamitin da ma’aikata kiwon lafiya suka yi wajen yaki da cutar a jihar.

“Muna kuma mika godiyar mu ga kamfanin Garment factory da suka taimaka wajen yin takunkumin fuska da kayan kariya wanda ma’aikatan lafiya suka rika amfani da su.

Gwamnan ya baiwa kwamitin yaki da cutar gudunmawar naira miliyan 30 domin inganta aiyukan da suke yi na hana yaduwar cutar da a jihar.

Share.

game da Author