Wasu daga cikin hadiman mataimakin gwamnan jihar Kwara Kayode Alabi sun kamu da cutar coronavirus.
Alabi wanda shine shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus na jihar Kwara ya Sanar da haka da yake zantawa da manema labarai ranar Lahadi.
Ya ce wadannan mutane na killace a asibitin kula da masu fama da cutar a Ilorin.
Alabi ya gargadi mutanen jihar su kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar kamar yadda hukumar sa ta rika yin shela akai.
Mutum 330 Suka kamu da kwayoyin cutar Korona a jihar Kwara, daga ciki 139 na kwance a asibiti, an sallami 179 sannan 12 sun mutu.
Wannan sanarwa ya fito ne kwanaki kadan da rasuwar shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar, Abdulrahman Abdulrazaq a dalilin fama da da yayi da cutar coronavirus.
Abdulrazaq ya rasu awowi kadan bayan an gabatar da sakamakon gwajin jinin sa da aka yi da ya nuna cutar yake ta fama da ita.
Kafin Abdulrazaq ya rasu ya rike mukamin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati daga ranar 7 ga watan Yuni 2019 zuwa rasuwarsa.
Gwamnatin jihar ta bada kwanakin bakwai domin yin zamammakoki da yin juyayin rasuwar Abdulrazaq.