HADARIN MOTA: ‘Yan sada 7 sun rasu a Kaduna

0

Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta bayyana cewa ‘yan sanda bakwai sun rasu a wani mummunar hadarin mota da aka yi a Jaji hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Frank Mba ya Sanar da haka a wani takarda da ya raba wa manema labarai ranar Talata.

Mba ya ce ‘yan sandan sun yi hadarin ne ranar Lahadi a hanyar su ta zuwa Katsina daga Kaduna.

Ya ce rundunar ta aika da jami’an tsaro 18 domin inganta yaki da mahara da masu garkuwa da mutane da ake fama da su a jihar Katsina.

“Hadarin ya auku a tsakanin wata mota kirar Tayota Hummer bus mai daukar fasinja 18 da wasu motoci.

” Jami’an mu 7 sun rasu a hadarin, 11 sun ji rauni. An kwantar da wadanda Suka ji rauni a asibiti a Jaji.

Mba ya ce Rundunar ta aika da likitoci domin duba wadanda suka ji raunin a asibitocin da aka kwantar da su.

Sufeto Janar din ‘yan sanda Mohammed Adamu ya yi juyayin rasa wadannan zaratan ‘Yan sanda da suka rasu yana mai cewa haka na daya daga cikin hanyoyin da jami’an tsaro ke sadaukar da rayukansu a dalilin aikin su.

Adamu ya ce an yi Jana’izar mutum 3 daga cikin 7 din da suka rasu da yake musulmai ne, sannan kuma ya umarci a biya iyalan mamatan dukkan hakkokin mazajen su cikin gaggawa.

Share.

game da Author