Gwamnatin Tarayya za ta kara tsaurara matakai don rage yawan mutanen da ke shiga asibitin fadar Aso Rock.
Babban sakataren fadar shugaban kasa Tijjani Umar ya sanar da haka ranar Alhamis.
Gwamnati ta yi haka ne domin inganta aiyukkan asibiti.
Umar ya ce bisa ga yadda tsarin yake kamata ya yi asibitin ta rika kula da kiwon lafiyar shugaban kasa da iyalensa, mataimakin shugaban Kasa da iyalensa sannan da ma’aikatan fadar shugaban kasa.
A 2015 gwamnati ta ware wa asibitin naira biliyan 3.94, daga nan asibitin ta samu naira biliyan N3.87 a 2016.
A shekaran 2017 gwamnati ta ware naira biliyan 331.70 sannan a shekaran 2018 asibitin ta samu naira biliyan 1.03.
A shekaran 2019 asibitin ta samu naira miliyan 800.
A dalilin haka ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya Sanar da Shirin da gwamnati ke yi wajen dawo da darajar da aka san asibitin da shi.
Kodinatan ‘Servicom National’ Nnennna Akajemeli ta bayyana cewa baya ga matsalar rashin kudi da asibitin ke fama da shi asibitin na fama da rashin isassun ma’aikatan lafiya musamman likitoci sannan da rashin wutan lantarki.
Bincike ya nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da iyalensa na daga cikin mutanen da ya kamata na samun kula a wannan asibiti amma basa zuwa.