Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya karbi cakin kudi na naira bilyan 162.557 domin ayyukan titina na cikin Kasafin Kudin 2020.
Wadannan zunzurutun kudi dai Ofishin Hukumar Kula da Basussuka ta Kasa ya samar da kudaden daga aljifan masu sha’awar zuba jari.
Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed ce ta wakilci Fashola wajen kwarya-kwaryan taron karbar cakin makudan kudaden.
Zainab ta ce babban makasudin bunkasa tattalin arzikin kasa, shi ne inganta hanyoyin da za su samar da matakan ci gaban yalwar arziki a kasa.
“A sakamakon haka ne Shugaban Kasa ya bayar da cifiko wajen bunkasa manyan ayyukan ci gaban kasa da suka hada da gina titina, hanyoyin jiragen kasa, ayyukan hasken lantarki da kuma bunkasa harkokin noma.
“Ofishin Kula da Basussuka ne ya samar da naira bilyan 162.557 daga masu sha’awar zuba jarin su a cikin watan Yuni, 2020. Kuma kudaden nan an samar da su ne kacokan domin aikin titina a karkashin kasafin kudade na 2020.
“Hakan kenan na nufin an samar da gaba dayan adadin makudan kudaden da aka yarda a kashe domin ayyukan titina a karkashin kasafin 2020.
Ta ce samar da wadannan kudade a karkashin Sukuk da aka yi, kwanan nan za a ga ayyuka baja-baja a kasar nan, tare da bunkasar yalwar arziki baki daya.
Fashola ya ce mutanen da ke zuba jari a karkashin tsarin Sukuk, su na yi ne domin sun nuna amincewa da yarda ga wannan gwamnati ta Shugaba Muhammadu Buhari.
“Ina tabbatar muku cewa yadda ku ka amince da mu har ku ka damka mana jarin ku domin a gina titina, to za mu yi aiki tukuru domin fita kunya. Yadda tsarin Sukuk na 1 da Sukuk na 2 suka yi nasara, to shi ma wannan Sukuk na 3 zai samar da gagarimar nasara wajen gina titina 44 da za a yi da wadannan makudan kudade.” Inji Fashola.
“Za a gina titina 8 a Arewa ta Tsakiya, titina 8 a Arewa maso Gabas, titina 7 a Arewa maso Yamma, titina 7 a Kudu maso Gabas, titina 10 a Kudu maso Kudu da kuma titina 6 a Kudu maso Yamma.” Inji Fashola.