Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da Shirin Noma Don Samar Da Abinci Da Aikin Yi (AFGP), wanda wani reshe ne daga shirin Tabbatar Da Dorewar Tattalin Arziki.
wannan shirin noma an kaddamar da shi ne domin rage wa manoma kuncin rayuwa sanadiyyar bullar cutar Coronavirus.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Ministan Harkokin Noma, Sabo Nanono, a lokacin da ake kaddamar da shirin a Katsina.
Sanarwar da kakakin yada labarai na Ma’aikatar Gona, Ezeaja Ikemefuna, ya fitar a ranar Alhamis,
“Wannan shiri zai magance kuncin rayuwar da mutane suka shiga sakamakon barkewar cutar Coronavirus a kasar nan da ma duniya baki daya.
“Shirin kuma zai kara zaburar da manoma hanyoyin bunkasa abinci, gyara shi da kuma hanyoyin sufurin sa a Najeriya.’
Minista kamar yadda aka ruwaito, ya ce, “wannan taron kaddamar da shiri ya na wakiltar sama da kananan manoma sama da su 1, 100,000 a fadin kasar nan.
Ya ce wadannan adadin kananan manoma sama da milyan 1, 100,000, suna cikin Rukunin Manoma na A ne da ke karkashin kamfanoni 6 da suka hada da AFEX, BabanGona, Value Seeds, Universal, Thrive Agric da kuma Oxfam.
“Nan ba da dadewa ba kuma za mu bayyana rukuni na biyu na B, na wadanda za su ci moriyar wannan shiri na noma.
Nanono ya tunatar yadda Shugaba Muhammdu Buhari ya kafa Kwamitin Farfado da Tallalin Arziki daga nakasun da ya samu bayan barkewar cutar Coronavirus.
Ya ce daya daga cikin hanyoyin farfado da tattalin arzikin kasar nan, har da Shirin AFJP, tare da cewa shirin zai bunkasa noma daga kasancewar sa noman tara abincin hannu-baka-hannu-kwarya zuwa na zamani kuma mai samar da wadataccen abinci.
Ya ce shirin dai ya kunshi shirin da gwamnati ta yi na raba abinci metrik tan na abinci har 100,000 ga shirin tsamo marasa galihu daga jigatar karancin abinci da yunwa a lokacin bullar cutar Coronavirus.
Ya ce a cikin shekara daya ana sa ran wannan gagarimin shiri, zai sanar wa matasa milyan 5 zuwa milyan 10 aiki.
Kuma zai samar da abinci kimanin metrik tan milyan 10 a hekta daga 20,000 zuwa 100, 000 a kowace jiha, ga manoma akalla milyan 2.4.