Gwamnatin Tarayya ta sanar da fara daukar kananan ma’aikata 774,000 da ta yi alkawari tun a farkon wannan shekara.
Gwamnati zata dauka matasa 1000 daga kowacce Karamar hukumar Kasar nan.
Latsa nan don sanin yadda zaka ka yi rajista
https://specialpublicworks.gov.nghttps://twitter.com/NigeriaGov/status/1282992408574164992?s=20
Idan ba a manta ba an Yi ta Kai ruwa Rana tsakanin karamin ministan kwadago da ‘yan majalisar dokoki ta Tarayya bisa yadda za a yi rabon guraben aiki.
Keyamo ya zargi Sanatoci da kokarin yin babakeren kwace yawan da za a dauka, duk kuwa da cewa an ba su alfarmar kawo wadanda za a dauka aikin har adadin kashi 15% daga cikin 774, 000 da za a dauka aikin.
Sanata Ubah ya ce Sanatoci ba su yi laifi ba don sun tambayi yadda aka raba daukar ma’aikatan.
A matsayi na na sanatan da ke wakiltar jama’a, hakki na ne na binciki yadda ya ke tafiyar da tsarin daukar ma’aikata a kasar nan. Saboda abin ya shafi wadanda na ke wakilta. Sannan kuma wanda aka damka wa aikin daukar ma’aikatan ba cikakken Minista ba ne, na je-ka-na-yi-ka ne.
“Ni ban san abin da Minista ke nufi ba, da ya yi kane-kane wajen daukar ma’aikatan da za a rika biya ladar naira 20,000 ko 30,000 a wata ba. In banda dan tasha da dan jagaliya, ya daga mun yi maka tambaya za ka kama cika ka na batsewa, ka na ihu da kwaratsatsa?
“Mu ne ya kamata a bai wa damar dauka ko kawo sunayen wadanda za a dauka.
“Amma damka aikin a hannun dan jagaliya da zai je ya yi harkallar raba guraben ayyukan, abu ne da ba za mu amince ba.”