Ministan Ayyuka Babatunde Fashola, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na kan aikin gyaran gadoji 37 a fadin kasar nan, cikin har da zungureriyar gadar da ta ratsa Lagos, wato Third Mainland Bridge.
Fashola ya furta haka, a taron manema labarai domin sanar da rufe wani sashe na gadar Mainland Bridge da za a yi domin ci gaba da gyara.
Ya ce ana ci gaba da gyaran gadojin da dama a yayin da masu motoci ba su daina zirga-zirga a kan su ba.
“Saboda Lagos ke tsohon babban birnin Najeriya, kuma birnin da ke gefen teku, sannan kuma akwai tsibirai a cikin birnin, shi ya sa ya ke da yawan manyan gadoji a kasar nan.
“A Lagos akwai manyan gadoji irin su Doma Bridge, Ojuelegba Bridge, da Kuma Independence da Faloma Bridge.
Daga nan sai ya ci gaba da zayyana irin ayyukan da ake kan yi a kan gadar Marine zuwa Apapa, kan gadar Eko da ta Obalende.
Ya ce gwamnati ta kididdige kudin aikin da Gadar Cara za ta ci, bayan lalacewar da gadar ta yi, sanadiyyar faduwar da wata mota tanka dauke da fetur ta yi a kan gadar.
Fashola ya bayyana sauran gadojin da ya ce gyara ya bi ta kan su, sun hada da Gadar Tatabu a Jihar Neja, Gadar Tamburawa a Kano, sai kuma tsohuwar Gadar River Neja da ta hade da Onacha da Asaba.
Sauran gadojin su ne Gadar Isaac Boro a Fatakwal, Gadar Etuck da ta hada Benin da Sapele, Gadar Katsina Ala a Benuwai, sai kuma Gadar Murtala Mohammed da ke Koton Karfe, Jihar Kogi.
Ya ce Gadar Third Mainland da za a rufe wani sashen ta a yanzu, an taba yi mata aiki cikin 2018 da 2019.
Ya ce aikin gyaran gadar zai dauki tsawon watanni hudu, daga ranar 24 Ga Yuli zuwa Janairu, 24 Ga Janairu, 2021.
Ya roki masu ababen hawa su bada hadin kan wannan gagarimin aikin da za a fara.