Hukumar Tace Finafinai ta Kasa (NFVCB), ta bayyana cewa ta san duk hanya da matakin da za ta iya dauka, matsawar wadanda suka shirya wani sabon fim da za a fitar da shi kwanan nan a kan ‘yan luwadi da madigo ba su kai shi Hukumar NFVCB din ta duba shi domin su tacewa kafin su sake shi kasuwa ba.
Shugaban Hukumar Adebayo Thomas ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa duk wani fim da za a fitar tilas a kai kwafen sa a hukumar domin a duba.
“Saboda dokar Najeriya ta hana nuna wasu abubuwa a cikin finafinai.” Inji Thomas.
“Muddin dai a Najeriya aka shirya fim din kuma ‘yan Najeriya ne, to duk inda suke sai mun gano su kuma sai mun kama fim din.”
“Idan ka ce ka na shirya fim a kan ‘yan madigo, ba mu da wata matsala da kai, har sai kwafen fim din ya zo hannun mu tukunna. Idan ya zo ne, sai mu duba mu gani. Idan akwai inda ya kauce wa abin da doka ta ce, sai mu nuna mu ce a cire. Idan kuma babu, shikenan.
‘Ife’: Yadda Fim Din ‘Yan Madigo Ya Tayar Da Kura Tun Kafin Ya Fito
Wannan fim mai suna Ife, labarin wasu mata biyu ne ‘yan madigo, da suka afka cikin zazzafar soyayya a cikin tsakanin su. Sun fuskanci kalubale a cikin al’ummar da suka taso a cikin ta, a Najeriya.
Wani darakta ne mai suna Uyai Ikpe-Erim ya bada umarnin fim din, wanda suka ce makasudin shirya fim din domin a dakushe mummunar fahimtar da ake yi wa ‘yan madigo, luwadi, ‘yan daudu, mata-maza a cikin Nollywood.
Furodusar fim din mai suna Pamela Adie, ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa bada labarin ‘yan madigo a cikin fim, ba wai ya na nufin haka a fili ‘yan fim din suke ba.
Ta ce akwai labarin bayarwa wanda ya kamata al’umma su sani dangane da rayuwar ‘yan madigo.
“Labaran da mu ke ji da gani a finafinai duk na wandanda ke bayyana irin tsanar mu da ake yi ne. Wani lokaci a dake mu ko ma a kashe mu. Ya kamata a sani cewa can mu ma fa mutane ne kamar kowa.” Inji Pamela.