Gwamnati ta ce za a fara jarabawar WAEC ranar 17 ga Agusta. Sannan kuma ajujuwan karshe a makarantun kasar nan za su koma ranar 5 ga Agusta.
Kakakin ma’aikatar ilmi, Ben Gooong, ya bayyana wannan shawara na gwamnati a sanarwa da ya fitar ranar litinin.
Ben Gooong ya ce ‘yan aji shida za su koma makaranta sati biyu kafin a fara jarabawar.
Idan ba a manta ba, ministan Ilmi ya bayyana cewa daliban Najeriya ba za su yi jarabawar ba a bana saboda karin yaduwar Korona da ake samu a jihar.
Yadda iyaye suka tursasa gwamnati ta canja shawara
Kungiyar Makarantu masu Zaman kansu da na Iyayen Dalibai sun nuna rashin amincewar su ga hukuncin da ministan Ilmi Adamu Adamu ya yanke na dakatar da yin jarabawar WAEC a Najeriya.
Shugaban Kungiyar Makarantu masu Zaman kansu ta Kasa, NAPPS, Yomi Otubela ya bayyana cewa lallai wannan gurguwar shawara ce ministan Adamu ya dauka domin kuwa su Makarantu masu Zaman kansu a shirye suke domin tabbatar da an bi dokar hukumar NCDC a lokacin da za a rubuta jarabawar.
” Dukka Makarantu masu Zaman kansu a sun shirya tsaf, za su samar da yanayin da ya dace a lokacin da dalibai suka fara zana jarabawar. Muna rokon ministan ya canja wannan matsayar tasa ya bari a rubuta jarabawar kamar yadda WAEC ta shirya kuma ta tsara.
Shima shugaban kungiyar Iyayen dalibai na Najeriya,Haruna Danjuma ya soki wannan matsayar na gwamnati.
” Akwai rudani cikin wannan hukunci da ministan ya yanke game da zana jarabawar WAEC din. Idan ba a manta ba kwamitin shugaban Kasa ta ce za a iya bude makarantu domin daliban ajin karshe su rubuta jarabawar WAEC din. Amma kuma kwatsam sai gashi ministan Ilmi ya fito ya some wannan umarni na kwamitin shugaban Kasa.
” Abinda ya kamata su gwamnati ta sani shine idan banda Turanci, Lissafi da Biology, babu wani jarabawa da zai Tara dalibai da yawa a wuri daya. Wasu ma darussan kamar Geography, Government da sauransu ba za a samu dalibai fiye da 40 ba.
” Kuma ma dai idan har za a yarda a bude kasuwanni, Masallatai, Otel ad wasu wuraren da ke tara jama’a me zai hana a bari yara su rubuta jarabawar karshe ba. Sannan kuma a haka aka rubuta jarabawar JAMB, duk ba a samu matsala ba sai WAEC.
Ita ko hukumar WAEC ta bayyana cewa tana aiki me a kasashe biyar dake yankin Afrika ta Yamma, kuma tare da hadin guiwar gwamnatocin wadannan kasashe.
” Ba za mu iya yin gaban Kan mu ba game da wannan matsala, dole sai mun shawarci kasashen da muke aiki a ciki da kuma matsayar gwamnatocin su kafin mu iya daukar matsayar a Kan abinda muka da a gaba.