Gwamnatin Kaduna ta kaddamar da wurin killace masu Korona mai gado 30 a Jema’a

0

Gwamnatin Kaduna karkashin gwamna Nasir El-Rufai ta maida cibiyar lafiya ta Kwalejin Koyan aikin Nas da Ungozoma dake Kafancan wurin killace wadanda suka kamu da cutar Korona.

A wannan wuri ne za a rika killace duk wanda ya kamu da cutar a yankin Kudancin Kaduna.

An samar da gadaje, kayan sawa na kariya, manyan likitocin, motocin daukar marasa lafiya da magunguna.

Babban Darektan Asibitin Kafancan Samuel Kure ya zazzagaya da shugaban Karamar Hukumar Jema’a Peter Averik ciki da wajen asibitin.

Akwai marasa lafiya biyu dake kwance a wannan wurin killace marasa lafiya dake fama da Korona.

Akarshe, shugaban karamar hukumar Jema’a Averik, ya godewa gwamna Nasir El-Rufai bisa wannan kokari da yayi na samar da wajen killace masu Korona a yankin kudancin Kaduna.

Share.

game da Author