A wata sanarwa da gwamnatun Kaduna ta yi, ranar Alhamis, gwamnati ta janye dokar hana sallar idi.
Mutanen Kaduna za su gudanar da sallolin idi sai dai kuma babu bukukuwa da za a yi sannan za a yi a waje ne cikin kiyaye sharuddan NCDC.
Ana sa ran za a yi babban sallah ranar Alhamis mai zuwa.
Har yanzu akwai dokar hana salloli a masallatan jihar.
Gwamnati a watan jiya ta janue dokar hana sallar Juma’a a jihar da zuwa Coci ranar Lahadi.
Jigar Kaduna na daga cikin jihohin da annobar Korona ke fantsama a kullum.
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 604 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Alhamis.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –203, Oyo-87, FCT-79, Edo-41, Osun-35, Ogun-24, Rivers-22, Kaduna-22, Akwa Ibom-20, Filato-18, Delta-9, Ebonyi-9, Imo-8, Enugu-5, Kano-5, Cross River-5, Katsina-4, Nasarawa-3, Borno-2, Ekiti-2 da Bauchi-1.
Yanzu mutum 38,948 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 16,061 sun warke, 833 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 22,054 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 14,009 FCT – 3,376, Oyo – 2,306, Edo – 2,105, Delta – 1,453, Rivers –1,587, Kano –1,452, Ogun – 1,227, Kaduna – 1,289, Katsina –717, Ondo – 1001 , Borno –605, Gombe – 558, Bauchi – 535, Ebonyi – 724, Filato – 780, Enugu – 726, Abia – 527, Imo – 462, Jigawa – 322, Kwara – 707, Bayelsa – 326, Nasarawa – 292, Osun – 394, Sokoto – 153, Niger – 166, Akwa Ibom – 196, Benue – 294, Adamawa – 115, Anambra – 132, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 64, Ekiti – 88, Taraba- 54, Kogi – 5, da Cross Rivers – 31.
Hanyoyin guje wa kamuwa da cutar covid-19
Kwayoyin cutar Corona Virus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.
Shi cutar akan kama shi ne a dalilin cudanya da dabbobi domin sune ke dauke da ita. Sakamakon bincike da aka yi game da cutar ya nuna cewa akan kamu da cutar ne ta hanyar yin muamula da dabbobi na gida da na daji.
Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.
Haka kuma idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.
1. A yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu
2. Za a iya amfani da man tsaftace hannu wato ‘Hand sanitizer’ domin tsaftace hannu idan Babu riwa da sabulu
3. A rika rufe hanci da baki idan za ayi atishawa kuma tari
4. Wanke da dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai
5. Nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya musamman Kira ko Kuma tari
6. A Rika amfani da takunkumin fuska musamman idan za a fita ko Kuma ana cikin mutane
7. A gaggauta zuwa asibiti da neman magani idan ba a da lafiya
Discussion about this post