Ranar Asabar din nan ce gwamnatin Shugaba Muhammdu Buhari ta sallami tubabbun ‘yan Boko Haram su 601 zuwa gidajen su, bayan sun kwashe zaman watanni shida ana yi musu bitar wankin kwakwalwar kankare musu akidar ta’addanci a zukatan su.
An gudanar da dan kwarya-kwaryar bikin yaye su daga Cibiyar Kankare wa Boko Haram Akidsi Ta’addanci da ke garin Malam Sidi, cikin Karamar Hukumar Kwami, Jihar Gombe.
Ana ba su wannan horon nasihohi da koyar da sana’o’in hannu ne a karkashin shirin kankare akidar ta’addanci mai suna ‘De-radicalization Reintegration and Reorientation’, (DRR), a karkashin gagarimin shirin karbar tubar ‘yan Boko Haram, mai suna ‘Operation Safe Corridor’, wato ka yi saranda a kama ka ko ka kai kan ka, sannan ka tuba ba za ka kara ba.
Shugaban shirin Manjo Janar Bsmidele Shafa, ya ce wadannan 601 da za a sallama, su ne rukuni na 4 na gungun Boko Haram da aka sallama bayan sun tuba.
Ya ce su wadannan sun shafe watanni 6, tun cikin Disamba kenan aka yi musu rajista a sansanin, kuma aka horar da su kyawawan dabi’u.
“Asali su 606 ne, amma uku sun mutu a cibiyar sakamakon wani ciwo da suka yi fama da shi, tun kafin su yi saranda.
“An tsame daya daga cikin su, saboda wani dalili, kuma an kan tuhuma, daya kuma an tura shi asibitin tababbu.
“Guda 587 ne ‘yan Najeriya, sauran 14 kuma ‘yan kasar Nijar ne, sai na Chadi da kuma Kamaru.”
Wadanda suka tura wakilai kuma wakilan suka yi jawabai a wurin, sun hada da Babban Hafsan Tsaro na Kasa, Abayomi Olanisakin, Gwamna Babagana Zulum na Barno da kuma Ministar Harkokin Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Marasa Galihu, Sadiya Faruq.
Yadda ‘Yan Boko Haram 602 Suka Daukar Wa Gwamnatin Buhari Alkawarin Daina Ta’addanci
Makonni biyu da suka gaata ne PREMIUM TIMES ts buga labarin yadda tubabbun ‘an Boko Haram 602 suka daukar wa Gwamnati alkawarin tuba daga aikata ta’addanci.
Wasu ‘yan Boko Haram 602 ne suka tuba, kuma suka yi wa Gwamnatin Tarayya rantsuwa cewa ba su kara tsoma kan su a harkar ta’addanci.
Tsoffin ‘yan Boko Haram din wadanda suka kammala zaman horon wankin kwakwalwa domin yaye musu akidar ta’addanci a zukatan su da kuma saisaita su domin komawa su ci gaba da rayuwa cikin al’umma, sun yi wannan rantsuwar ta fandare wa Boko Haram da ta’addanci a Sansanin Malam Sidi da ke cikin Karamar Hukumar Kwami da ke Jihar Gombe.
Sun yi wannan rantsuwar daina ta’addanci da daukar alkawari ga Gwamnatin Najeriya a gaban wasu mambobi 11 na Kwamitin Shari’a a karkashin Mai Shari’a Nehizena Afolabi na Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe.
Da ya ke bayani a wurin daukar alkawarin, Kwamandan ‘Operation Safe Corridor’ ( Shirin Ka Yi Saranda Ka Tsira Da Ranka), Manjo Janar Bamidele Shafa, ya ce bayyanar tsoffin ‘yan ta’addar a gaban Kwamitin Alkalai na daya daga cikin sharuddan sallamar tubabbun Boko Haram din su koma gidajen su ko cikin sauran al’umma.
‘Bayyana Ta’addancin Da Ka Yi A Baya, Ka Tuba Ka Tafi Abin Ka’
“Wannan kwamiti ya na zama ne ya saurari bayanin ta’addancin da suka shuka kafin su tuba. Daga nan sai su ce sun tuba, kuma su dauki alkawarin cewa su da Boko Haram ko ISWAP har abada.
“Sai kuma su yi rantsuwa cewa sun dauki alkawari ga Gwamnatin Najeriya za su yi mata da’a da biyayya kuma da zama ‘yan kasa nagari.
“Sannan za su jaddada cewa za su fansar da duk wani ‘yanci da aka ba su idan suka sake yin wani laifi aka kama su.”
Wato idan aka sake kama su da laifi, to duk wani ‘yanci ko yafewar da aka yi musu da tubar su da aka karba, duk an shafe su, za a hukunta su.”
Manjo Janar Shafa ya ce tun bayan fara Shirin Wanke Zukata da Kwakwalwar ‘Yan Boko Haram, an dauki mutum 893 da suka tuba, kuma an maida mutum 280 ga hukumomin jihohin su. Wasu ‘yan kasar Chadi biyu kuma an damka su ga jami’an kasar bayan sun tuba daga ta’addanci.
Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Barno, Gambo Zuwaira, ta ce tuni a jihar akwai shiri domin dorawa daga inda wannan tsari ya tsaya.
“Tubabbu ‘yan jihar za su samu shawarwari daga gwamnati, nasiha da wa’azi. Sannan kuma za a ba su jarin fara sana’ar da kowanen su ya koya a sansanin da aka killace su, aka yi musu wankin kwakwalwa da kankare akidar ta’addanci a zukatan su.”
Ta ce daga cikin wadanda aka sallama a baya, akwai wanda ke samun har naira 250,000 duk wata daga sana’ar aski. Kuma har ma ya dauki wasu matasa aiki a karkashin sa.
Discussion about this post