Gwamnati tarayya ta janye umarnin da ta ba makarantu su koma domin daliban ajin karshe damar rubuta jarabawar WAEC.
Idan ba a manta ba gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za a fara rubuta jarabawar kammala babban Sakandare daga ranar 4 ga watan Agusta zuwa 5 ga watan Satumba.
Gwamnati ta ce da zarar an kammala wannan jarabawa sai kuma a maida hankali wajen yin jarabawar NABTEB da NECO.
Idan ba a manta ba gwamnatin tarayya ta umarci ‘yan aji shida na babban sakandare su koma makaranta domin shirin rubuta jarabawar WAEC.
Sai dai kuma a ranar Laraba, gwamnatin tarayya ta janhye wannan umarni na bude makarantun kasar da kuma rubuta jarabawar WAEC da ta ce za a yi a watan Agusta zuwa Satumba.
” Babu makarantar da za a yarda ta fara aikin don jarabawar WAEC. Gara ace dalibai sun rasa shekara daya na makaranta da ace sun afka hadadrin kamuwa da korona.
” Za a bude makarantu ne a lokacin da gwamnati ta gamsu cewa babu hadari ga yara, ba wai don hukumar shirya jarabawar WAEC ta shirya rubuta jarabawa ba.
” Ku duba ku gani, yau idan yaro daya ya kamu da Korona, zai yadawa yaran ajinsa cikin dan kankanin lokaci, haka kuma idan a dakunan kwanan dalibai ne cutar zata yadu kamar wutar daji. Tsakani da Allah, lokaci bai yi ba na bude makarantu. Yara fa ba su san bada tazara a tsakanin su ba.