Gwamnatin jihar Oyo ta soke zangon karshe na makarantun jihar.
Kwamihinan Ilmin jihar , Olasunkanmi Olaleye ya bayyana haka bayan taron kwamitin zartaswar jihar a madadin gwamnan jihar Seyi Makinde.
Olaleye ya ce gwamnati ta amince da soke zangon karatu na karshe a jihar. Cewa yara za su shiga aji na gaba ne ta hanyar yin amfani da gwajin da aka yi musu a zangon karatu na farko da na biyu.
Daga nan sai Olaleye ya bayyana sabon ranar da gwamnatin jihar zata bude makarantun jihar.
” Gwamnatin jihar za ta bude duka makarantun jihar ranar 21 ga Satumba domin fara sabon zangon Karatu.
Sannan kuma daliban dake ajujuwan karshe za su rubuta jarabawar zuwa ajujuwan gaba a cikin wasu ranaku da gwamnatin ta ambato.
A karshe kwamishinan ya ce daliban da ke ajin karshe na babban sakandare kuma za su jira shawarar da hukumar shirya jarabawa, WAEC tukunna.
Idan ba a manta ba gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta amince yara su rubuta jarabawar WAEC ba saboda karin yaduwar Korona da ake samu a Najeriya.
WAEC na cigaba da tattaunawa da gwamnatocin kasashe biyar da take shirya jarabawa a ciki domin daukar matsaya akan shirya jarabawar.
Discussion about this post