A ranar Litini ne Gwamna jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya sanar cewa sakamakon gwajin cutar da aka yi masa ya nuna cewa ya warke daga cutar coronavirus.
Akeredolu ya rubuta haka a shafin sa ta tiwita, sannan ya mika godiyar sa ga dukkan mutane da suka rika bin sa da addu’o’in Allah ya bashi lafiya a lokacin da yake kwance.
Sannan kuma gwamna Akeredolu ya kara da cewa har yanzu gwamnati bata na nada sabon kwamishinan kiwon lafiya ba cewa ai bashi shawara kan harkokin kiwon lafiya ne ke rike da ofishin kafin gwamnati ta nada wani sabo.
Ya ce gwamnati ta bude wurin yin gwajin cutar a asibitin gwamnatin tarayya FMC dake Owo domin rage yawan aikin da asibitin Akure ke yi a jihar.
Mutum 20 sun mutu a jihar a dalilin kamuwa da cutar Korona.
Mutum 472 sun kamu da cutar, daga ciki an sallami mutum 113.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda Akeredolu ya kamu da cutar coronavirus.
Bayan kwanakin da kamuwa da cutar kwamishinan lafiyar jihar Wahab Adegbenro, ya rasu a dalilin kamuwa da kwayoyin cutar.
A bisa haka Akeredolu ya umarci duk manyan ma’aikatan gwamnati da su gaggauta yin gwajin cutar sannan su killace kan su.
Duk da dai gwamnati bata fadi kai tsaye cewa cutar ce tayi ajalin kwamishinan ba, kwararan majiya sun shaida cewa Korona ce ta yi ajalin domin Adegbenro ya rasu a asibitin kula da masu fama da cutar a jihar.