Ganin cewa mafi yawan fyade da ake yi wa kananan ‘yan mata a Kano, yana faruwa ne a tsohon kangon ginin da ba a gama gina shi ba, gwamnatin Kano ta bada shelar cewa duk wani mai tsohon kangon gina a jihar ya gine shi ko kuma a daure shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Haruna ya bayyana haka ranar Alhamis.
Haruna ya ce a dalilin haka jami’an tsaro za su rika bin duk wani kagon gini dake jihar suna cafke wadanda ke boyewa ciki suna tafka barna.
” Duk wanda aka kama da laifin aikata wani mummunar abu a irin wani kangon gini, toh laifin zai shafi harda mai mallakin wannan gini.
Haruna ya yi kira masu irin wadannan gine-gine a jihar da su gaggauta gine su tun da wuri.
Sakamakon bincike
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa a tsakanin watannin Janairu zuwa Mayu 2020 an yi wa mata 42 fyade kuma duk suna gaban kuliya.
Sannan kuma akalla kashi 33.3 bisa 100 na aukuwa ne a ire-iren wadannan kangon gini da ba a kammala su ba.
Kashi 17.7 a gonaki, 15.6 a shaguna, 15.6 a dakuna sannan kashi 8.9 a makarantun kashi 2.2 kuma a kasuwani.
A karshe rundunar ta gargadi masu aikata irin wadannan laifuka da su shiga taitayin su domin hukumar ba za ta yi kasa-kasa ba wajen hukunta duk wanda aka kama da laifin aikata hakan.