Farashin danyen man fetur ya sake zubewa kasa, daidai lokacin da Korona ta sake darkakar Amurka

0

Farashin gangar danyen man fetur ya sake faduwa kasa, daidai lokacin da cutar Coronavirus ta sake waiwayawa baya, ta darkaki Amurka.

Wannan faduwar farashi tare da juyawar da Coronavirus ta kara yi kan Amurkawa, ya haifar da fargaba, musamman ganin cewa hakan zai takaita cinikin mai a Amurka, wadda ita ce ta fi kowace kasa tu’ammali da danyen mai a duniya.

Danyen man Amurka mai suna WTI ya yi kasa daga dala 40.79 zuws dala 40 46.

Shi kuma samfurin Brent ya yi kasa daga dala 43 19 zuwa 42.91.

Yayin da wasu jihohin Amurka 16 suka bada rahoton karin fantsamar Cutar Coronavirus a cikin su, akwai farga bar cewa matakan da hukumomin kula da lafiya za su dauka don dakile cutar, zai rage yawan masu amfani da danyen mai a Amurka da yawan gaske.

Haka dai Kamfanin Dillancin Labarai na Reauters ya ruwaito.

Jihar California da ta Texas, jihohi mafi l al’umma da kuma karfin tattali, sun bayyana karuwar masu kamuwa da cutar Coronavirus a ‘yan kwanakin nan.

Jihar Florida ta bayyana karin masu kamuwa tare da bayyana wasu matakai da dauka, wadanda za su kawo tawaya ga tattalin arziki da masana’antu.

Tsoron da masu nazarin danyen mai da faduwa da tashin farashin gangar sa ke yi zai kara haifar da matsala, musamman kuma idan aka dubi yiwuwar sake kulle jama’a a gida. Haka wani gawurtaccen Mai nazarin kasuwar danyen mai a duniya, maj suna Micheal McCarthy ya bayyana a birnin Sydney, ta wani i-mel da ya raba.

Share.

game da Author