FALLASA: Jonathan ko Buhari – wane dan kakuduba ne ya jinginar da Najeriya a yarjejeniyar gina Tashar Lantarki ta Azura?

0

Ranar Lahadin da ta wuce ne wani babban jami’in gwamnatin nan ya shaida wa ‘yan jarida a Abuja cewa, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya sa hannun yarjejeniyar amincewa da wata cukuikuyayyar kwangilar gina tashar wutar lantarki da Azura.

A cikin yarjejeniyar mai cike da sarkakkiya, kamfanin zai gina tashar samar da hasken lantarki mai karfin wuta miga wat 450 a Najeriya.

Jami’in gwamnatin wanda ba ya so a ambaci sunan sa, ya ce Jonathan ne ya sa hannun, domin tun daga ranar 23 Ga Afrilu, 2013 yarjejeniyar (Power Purchase Agreement, PPA) ta fara aiki, kafin Muhammdu Buhari ya hau mulki.

An watsa wannan ikirari da babban jami’in Fadar Shugaban Kasa ya yi a kafafen yada labarai da dama, ciki har da jaridar PUNCH.

Jangwangwamar Yadda Najeriya Ke Biyar Bilyoyin Nairori Ladar Kwangilar Da Ko Falankin Katako Ba A Buga Ba:

Kwangilar gida tashar lantarki ta Azura dai ta zama tonon sililin wata sabuwar harkalla ‘yan makonnin da suka gabata.

1. Takardun bayanan da suka fado hannun PREMIUM TIMES, sun nuna: Najeriya za ta biya Azura dala bilyan 1.2 idan har bayan rattaba hannun yarjejeniyar sai ta nemi ta fasa gina tashar, wato ta soke kwangilar (PPOP a Turance).

2. Tuni dama ta rattaba hannun yarda za ta biya dala milyan 30 zuwa dala milyan 33 a kowane wata ga kamfanin Azura. Wadannan ladar sa wutar ce, ko da kuwa an kunna makunni ba a samu harke ko da mai karfin hasken cocila an raba wa Kamfanin Rarraba Hasken Lantarki na Kasa ba (TCN).

3. Najeriya kuma ta na biyan naira milyan 700 duk wata matsayin kudaden cike gibin tashin farashin dala a Najeriya.

A Soke Kwangilar Azura, Cike Ta Ke Da Hatsarin Gaske -Majalisar Dattawa: Kwanan nan sai Majalisar Dattawa ta ce a soke kwangilar, saboda cike da ke da cinikin biri a sama.

Cikin Rahoton Kwamitin Lantarki na Majalisar Dattawa, wanda Shugaban Kwamitin, Sanata Gabriel Suswam ya ce kulla wannan yarjejeniyar tamkar an jinginar da arzikin Najeriya ga Azura.

Yadda Jonathan Ya Yi Cinikin ‘Balan-balan’ A Matsayin Tashar Lantarki A Hannun Azura:

Yarjejeniyar gina tashar lantarki da kamfanin Azura wadda da har yau ko diga da cebur ba a kai wurin aiki ba, ba a lokaci daya aka kammala sa hannun ta ba.

Farko: An sa hannun farko a karkashin amincewar Jonathan, tsakanin Kamfanin Sayar Da Lantarki na NBET Plc, a madadin Najeriya da kuma Azura Power West Afrca, a ranar 22 Ga Afrilu, 2013. Kuma a cikin Fadar Shugaban Kasa aka yi taron rattaba hannu a yarjejeniyar.

Jaridu sun buga labarin yarjejeniyar a lokacin, ciki har da Business Day.

Yarjejeniyar ta kuma nuna cewa Azura zai zuba dala milyan 700 wajen aikin ginin, wanda zai samar da migawat na wuta 1000, tare da samar wa mutum 1000 aiki. Kuma ana sa ran za a kammala har a fara amfana a cikin 2016.

Yarjejeniya Ko Dai Kitso Da Kwarkwata Cikin Kai?

Sai dai kuma wasu takardun bayanan da PREMIUM TIMES ta samu sun nuna cewa Ministan Shari’a na Lokacin, Adoke Mohammed, ya ki rattaba hannun amincewa yarjejeniyar ta zama doka. Saboda ya hango cewa an shirya wa Najeriya shigo-,shigo din da zai yi sanadiyyar tatsar kudin ta masu tsananin yawa, ko da kuwa ba a gudanar da aikin ba.

Adoke da Ministar Harkokin Kudade ta lokacin sun rika yin karakainar wasiku tsakanin su, da kuma tsakanin Adoke da Fadar Shugaban Kasa, ya na nuna musu hatsarin da Najeriya za ta shiga idan a matsayin sa na Ministan Shari’a ya sa hannu yarjejeniyar ta zama doka.

Adoke ya ce yarjejeniyar ka iya janyo kudaden da ke asusun ajiyar Najeriya na kasar waje su rika komawa aljihun kamfanin Azura.

Wasikar farko da Adoke ya rubuta, inda ya ce ya ki amincewa da yarjejeniyar, har sai an gyara wasu wuraren da ya nemi a gyara, ya rubuta ta ne a ranar 24 Ga Yuli, 2014.

Yarjejenia ta 13. 1.2 ce Adoke ya fi jajircewa a sake, inda ya nemi a cire inda aka ce: “Idan aka samu sabani to Najeriya ta sallamar tare da fawwala wa kotu umarnin a biya Azura hakkokin sa daga cikin kadarori ko kudaden shigar Najeriya.”

A karshe Adoke ya rubuta shawara ga Jonathan cewa ya umarci Okonjo-Iweala ta shigar da wuraren da ya nemi a gyara a cikin yarjejeniyar.

Bakin Alkalami Ya Bushe: Amma fa yarjejeniya ba ta kammalu ba tukunna.

PREMIUM TIMES ta gano cewa ba a kai ga yin wani abu ba, har ‘yan sauran watannin da suka rage wa Jonathan suka cika, ya fadi zabe Buhari ya hau mulki a ranar 29 Ga Mayu, 2015.

Yadda Buhari Ya Sa Hannu Cinikin ‘Goriba’ A Matsayin Tashar Wutar Lantarki:

An samu gagarimar matsala dangane da kwangilar tun daga ranar da aka rantsar da Buhari.

1. Bai nada Ministoci ba tun cikin Mayu sai cikin Nuwamba, ballantana ministoci su rika bibiyar tunatar masa da batun yarjejeniyar kan wuraren da ya kamata a yi wa kwaskwarima, kamar yadda Adoke ya rubuta cewa lallai a yi haka tun a zamanin Jonathan.

2. Wasu ‘yan kumumuwa sun rika matsa-lamba ga Buhari cewa ya sa hannun amincewa ga aikin ginin tashar lantarkin, duk kuwa da cewa babu ministoci.

4. Buhari ya sa hannun amincewa a ranar 21 Ga Agusta, 2015, cewa a gina Azura-Edo Independent Power Plant mai karfin wuta migawat 450.

Yanzu haka PREMIUM TIMES ta mallaki kwafen wannan yarjejeniya a hannun ta.

GASKIYAR MAGANA: Ikirarin da jami’in Fadar Shugaban Kasa ya yi cewa Goodluck Jonathan ne ya sa hannu a kwangilar, ba gaskiya ya furta ba.

Shi kan sa Shugaban Kwamitin Makamashi, Sanata Suswam a takardar da ya karanta, ya tabbatar da haka.

BINCIKEN PREMIUM TIMES: BUHARI ne ya sa wa yarjejeniyar hannu.

Share.

game da Author