Duk da irin wannan fantsama da annobar Korona ke yi tare da kisa a duniya, akwai milyoyin mutane har a nan Najeriya da ba su yi amanna cewa akwai cutar ba.
Yadda Korona ta kama sama da mutum milyan 16 cikin wata 7
1. Makonni 15 bayan farkon bullar cutar, adadin wadanda suka kamu a duniya sun kai mutum milyan 2.
2. Zuwa ranar 13 Ga Yuli, ta kama mutum milyan 13 a duniya.
3. Kwanaki 5 bayan adadin ya kai milyan 13, ta kara kama mutum milyan 2, yadda adadin ya haura mutum milyan 15 a ranar 21 Ga Yuli.
4. Zuwa rubuta wannan labari, mutum milyan 16, 202,385 suka kamu a duniya.
5. Wadanda cutar ta kashe zuwa wannan rana sun kai mutum 650,000.
6. Korona ta fi yin mummunar illa a kasashe hudu na duniya: Amurka, Brazil, Rasha da Indiya.
7. Korona ta kama mutum milyan 4, 315,709 a Amurka; sama da mutum milyan 2.3 a Brazil, mutum 806, 720 a Rasha, sai mutum sama da milyan 1 a Indiya.
8. Mutum milyan 9 da cutar ta kama daga milyan 16 da Korona ta kama da duniya, duk a kasashen Amurka, Barazil da China suke. Kusan rabin wadanda ta kama a duniya kenan.
9. Korona ta kama mutum 40,000 a ranar Juma’a, a kasar Indiya a rana daya kenan.
10. Mutum milyan 9, 919,232 suka murmure bayan Korona ta kwantar da su a duniya.
11. Sama da mutum 800,000 Korona ta kama a Afrika.
12. Korona ta kashe sama da mutum 17,000 a Afrika baki-daya.
13. A Afrika ta Kudu Korona ta fi yin mummunar illa a nahiyar Afrika. Mutum 432, 200 suka kamu, a cikin su ta kashe mutum 6,655.
Discussion about this post