Fadar shugaban Kasa ya bayyana cewa dalilin da ya sa zaman lafiya ya gagara tabbata a yankin kudancin Kaduna shine yadda aka maida ta’addanci wani salo na siyasa, kashe-kashe ta hanyar kabilanci da ramuwar gayya a tsakanin mutane.
Rayukan daruruwan mutane sun salwata a dalilin hare-haren ta’addanci a yankin a shekarun da suka wuce. Irin wannan kashe-kashe yayi tsani duk da jibge dakarun sojoji da gwamnatin tarayya ta yi a yankin.
” Ba kamar wasu yankunan kasar nan dake fama da hare-haren ta’addanci ba, salon na yankin kudancin Kaduna da bam yake.
” Ya tabbata daga bayannan dake kasa cewa kashe-kashen yankin kudancin Kaduna ya karkata ne ga yadda aka maida ta’addanci wani salo na siyasa, kashe-kashe ta hanyar danganta rikici da kabilanci ko addini da ramuwar gayya a tsakanin mutane.
” Wani dan ta’adda zai farwa irin sa dake ba kabila ko addinin su daya ba. Hakan sai a dauka kuma su a bangaren da aka kashe suma su far wa wadancan bangaren, sai kuma a jefa addini da kabilanci a ciki. Wannan ya kai hari, daga baya wancan bangaren suma su dau fansa.
Akarshe fadar gwamnati ta hori jama’a da su daina daukar doka a hannun su. Maimakon haka su rika sanar da jami’an tsaro dake jibge a wannan yanki.
Fadar gwamnatin Buhari ta jajanta wa mutanen yankin da aka kashe a harin kwana-kwanan nan a Igali, Birnin Gwari da Giwa.