Dalilin da ya sa na fice daga PDP – Yakubu Dogara

0

Tsohon shugaban majalisar Tarayya, Yakubu Dogara ya bayyana wasu dalilai da ya sa ya fice daga PDP ya koma APC.

Idan ba a manta ba Tsohon Shugaban Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara ya wancakalar da jam’iyyar PDP, ya koma APC a cikin wannan mako.

Dogara ya bayyana haka ne bayan ganawa da yayi da shugaban Kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnati ranar Juma’a.

A shekarar 2018 Dogara ya fice daga jam’iyyar APC ya koma PDP, bayan rashin jituwa da ya shiga tsakanin su da gwamnan jihar a wancan lokaci.

Idan ba a manta ba tare suka hada kai da gwamnan Bauchi, Bala Mohammed , suka kada APC a jihar Bauchi.

Dogara ya ce da ya tsaya yana shan wulakancin gwamna Bala na PDP a jihar Bauchi da ya taimaka wa matuka ya yi nasara a zaben 2019, gara ya tattara ya fice daga jam’iyyar ya koma inda ya APC.

” Babban dalilin da ya sa na fice kiwa shine yadda PDP ke mulki a jihar Bauchi.

” Kowa ya san irin rawar da na taka a zaben gwamnan jihar wanda tsohon ministan Abuja, Bala Mohammed ya doke gwamna mai ci, Mohammed Abubakar.

” Amma kuma yanzu nine abin watsarwa da cakala a gwamnatin Bala. Maimakon in ci gaba da zama a PDP ana min abinda aka dama gara a kauce in basu wuri, in koma inda na fito.

Dogara ya rubuta wasikar fice wa daga PDP wanda ya aika wa shugaban jam’iyyar na mazabar sa, Bogoro C, dake jihar Bauchi.

A karshe ya ce kamar yadda ya rika nunawa sauran gwamnoni inda suka gaza da inda za su gyara a baya, shi kuma Bala ba shafaffe da mai bane. Gara in yi tafiyata in kyale su.

Share.

game da Author