DA WALAKIN GORO A MIYA: A bincike jiga-jigan PDP da aka gansu dumu-dumu da kasurgumin dan Damfara – APC

0

Jam’iyyar APC ta yi kira ga jami’an tsaro da su tuhumi wasu daga cikin jiga-jigan PDP a dalilin alaka da suje da shi da kasurgumin dan damfara, Ramon Abbas.

APC, ta kara da cewa an rika ganin hotunan Ramon da aka fi sani da Hushpuppi, tare da jiga-jigan PDP kamar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsohon kakakin majalisar tarayya, Yakubu Dogara, Sanata Dino Melaye da dai sauran su.

APC ta ce, tabbas da walakin goro a miya, ganin cewa a kullum ‘yan PDP za su shirya wani makircin su ta siyasa, kaji su sun garzaya Dubai, ashe akwai wani abin da suke boyewa. Jam’iyyar ta ce lallai a bincike su.

Martanin PDP

Jam’iyyar PDP ta bayyana kiran da APC ta yi kan a tuhumi wasu manyan PDP da ta ce su na da alaka da dan 419 Hushpuppi, cewa rashin mutunci ne da rashin kamun-kai.

PDP ta ce hakan ya nuna irin bakar aniyar kuncin zuciyar da ‘yan APC ke fama da shi, sai kuma kududun bakin ciki da mugun nufin bi-ta-da-kulli kan ‘yan adawa.

Cikin wata sanarwa da Kakakin APC na Kasa, Kola Olagbondiyan ya fitar, ya ce “wannan mummunan zargin da APC ta yi, ya nuna yadda jam’iyya mai mulki ke kitsa karya da sharri da tuggu a kan masu adawar da ba su ji ba, ba su kuma gani ba, jam’iyyun adawa da duk masu ra’ayin da ya sha babban da na gwamnatin APC, ta na bin su da kazafi da sunan wai yaki da cin hanci da rashawa.”

Cikin wadanda APC ta ce a kama a tuhume su, har da Atiku Abubakar, Bukola Saraki, Yakubu Dogara da kuma Dino Melaye.

Jami’an tsaro sun damke Hushpuppi da aka sani da Raymond Abbas a Dubai, daga nan aka aika shi Amurka, a hannun jami’an FBI.

Sharrin Da APC Ta Fara, Alamomin Tuggun 2023 Ne -PDP

PDP ta ce kokarin da APC ke yi ba wani abu ba ne sai fara shirya wa ‘yan adawa gadar-zare domin su rufta tunk kafin zaben 2023 ya gabato.

“Jami’an tsaro na FBI da Dubai duk sun yi binciken su, ba su ce sun samu wani dan PDP da laifi tare da Hushpuppi ba. Sai APC gungun masu rashin mutunci da rashin ta-ido ne za su nemi kitsa wannan sharri.

PDP ta ce in dai daukar hoto ne da wani da ake zargi don ya yi da Atiku Abubakar zai say danganta shi da mai laifi, to Shugaba Muhammadu Buhari ma ya yi irin wannan hotuna.

Me ya sa APC ba ta nemi an binciki Ganduje ba? – PDP

“In banda rashin ta-ido, me zai hana APC ta nemi a binciki wani gwamnan ta da aka nuna wa duniya tulin fayafayen bidiyon da ya ke cuc-cusa milyoyin daloli a cikin aljifan sa ba?

“Kuma don me ba ta sa an binciki dan takarar ta na zaben gwamnan Edo Mai zuwa ba. Wanda Shugaban APC da kan sa ya kira shi “barawo, wanda ba shi da wani amfani wajen shugabancin al’umma, sai dai a yi amfani da shi wajen kitsa tuggun siyasa a tsakiyar talatainin dare.”

PDP ta kalubalanci APC cewa jam’iyyar da gwamnatin da ta kafa sun shiririce, sun zama dibgsggun da rikicin shugabanci ya kidimar da su, sun danka jam’iyya a hannun gwamna, sun bar al’ummar Najeriya a hannun Boko Haram, mahara da sauran ‘yan bindigar da ke kashe jama’a a kowace rana.

Share.

game da Author