Babban bankin Najeriya CBN ya karya darajar naira, yanzu dala daya zai tashi akan naira 381, canjin banki.
Ko da yake bankin bai sanar da canjin da aka samu ba, canjin ya bayyana a kasuwar hada-hadar kudi.
Hakan ya nuna cewa yanzu canjin naira ya tashi daga naira 360 zuwa naira 381 akan dalar Amurka daya.