Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Tukur Buratai, ya yaba wa shirin ganin zaman lafiya ya sake wanzuwa a Jihar Zamfara, wanda Bello Matawalle, Gwamnan Jihar ke aiwatarwa.
Buratai ya bayyana haka a lokacin da Matawalle ke zagayawa da shi cikin daya daga rugage uku da jihar ke ginawa, domin tsugunar da tubabbun ‘yan bindiga.
An dai kusa kammala ginin ruga ta farko a yankin Maradun, wadda ta kunshi fadin hekta 2,500. Kuma za ta kunshi filin kiwo, gidajen kwana, makaranta, asibiti, asibitin dabbobi, madatsun ruwa da tafkuna, hanyar magudanun ruwa, ofishin ‘yan sanda, titina, filayen wasa da kuma masallatai.
Yayin da ya ke gane wa idon sa yadda aikin wurin ya fara kankama, Buratai ya ce lallai Gwamna Matawalle tauraron jaddada zaman lafiya ne, kuma ya na kira duk wani mutumin kwarai na Jihar da ya mara masa baya, domin ganin an kakkabe mabarnata a jihar.
Ya kuma yi alkawarin cewa sojojin Najeriya za su goya masa baya a koyaushe domin tabbatar da samun dawwamammen zaman lafiya a Zamfara.
A fadar Sarkin Maradun Muhammadu Tambari kuwa, Buratai ya shaida wa Sarkin Kayan Maradun cewa su na da abin alfahari a matsayin dan su, wanda ke Gwamna a Zamfara.
Tambari ya gode da ziyarar da Buratai ya kai, kuma ya kara shan alwashin cewa za su ci gaba da goyon bayan shirin sojoji domin tabbatar da zaman lafiya, kamar yadda tun farko ya yi wa gwamnatin Matawalle alkawari.