Buhari ya zarce shugabannin kasashen Afrika kaf a yawan mabiya a shafin Tiwita

0

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ne shugaban da aka fi yin muamula da kuma ya fi yawan mabiya cikin shugabannin kasashen Afrika kaf din su a shafin Tiwita.

Haka sakamakon rahoton Twiplomacy ya nuna.

Buhari na da mabiya miliyan 3,121,169 da suke bin sa a shafin tiwita.

Daga Buhari sai shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame, dake da mabiya 1,910,159.

Bubari ya bashi ratar mutum sama da Miliyan daya.

Shugaban kasar Afrika Ta Kudu Cyrul Ramaphosa ne na uku a yawan mabiya a tiwita da mabiya 1,386,849.

A duniya kuma, shugaban Amurka Donald Trump ne ya fi yawan mabiya a shafin tiwita a duniya cikin shugabannin duniya kaf.

Trump na da mabiya 81.1, daga shi sai shugaban kasar India, Narendra Modi, dake da mabiya 57.9.

Pope Francis ne na uku a duniya da mabiya sama da mabiya miliyan 51.

A nahiyar Turai kuma shugaban kasar Faransa ne ke kan gaba da mabiya 5,293,346

Daga Macron sai shugaban Spain Pedro Sánchez, dake bi masa da mabiya 1,405,481.

Share.

game da Author