Buhari ya yi tir da harin jirgin Majalisar Dinkin Duniya da Boko Haram suka yi

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Alla-wadai da harin da Boko Haram suka kai kan helikwafta mallakar Majalisar Dinkin Duniya a Barno.

Sun kai wa jirgin hari ne a wani farmaki da suka kai a Damasak, a ranar Alhamis, inda suka kashe mutum biyu, cikin su kuwa har da yaro mai shekara biyar. Haka UN ta bayyana.

“Direban jirgin ya yi nasarar ci gaba da tuka jirgin zuwa Maiduguri, duk kuwa da cewa harsahi ya samu jirgin.

“Babu ma’aikatan agaji a cikin jirgin, a lokacin da aka harbe shi, kuma sauran matukan jirgin duk lafiyar su kalau.”

Majalisar Dinkin Duniya ta ce direban ya yi tafiyar kilomita 150 da jirgin zuwa Maiduguri, bayan an harbi jirgin.

Edward Kallon wanda shi ne kodinatan ayyukan agaji na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, shi ne ya tabbatar da afkuwar lamarin.

“Harin da Boko Haram suka kai wa jirgin Majalisar Dinkin Duniya har suka kashe mutum biyu, abin Allah wadai ne. Kuma ina tabbatar da cewa wadanda suka kai wannan harin za su yaba wa aya zaki.” Inji Buhari, cikin wata sanarwa da kakakin yada labaran sa Garba Shehu ya fitar.

Buhari ya kara jaddada cewa karyar Boko Haram ta rigaya ta kare, an karya lagon su. Su na kai wa fararen hula hari ne kawai don a rika ganin kamar su na da wani karfin yin mummunan tasiri.

PREMIUM TIMES ta buga labarin kai hari makamancin wannan a wani sansani na Majalisar Dinkin Duniya a Ngala, cikin watan Janairu.

Share.

game da Author