BOKO HARAM: Manjo Janar da ya yi korafin karancin makamai na fuskantar tuhuma a asirce

0

Tsohon kwamandan Rundunar Operation Lafiya Dole masu yaki da Boko Haram, Manjo Janar Olusegun Adeniyi, zai fuskanci tuhuma a asirce, kamar yadda wata majiya ta sanar wa PREMIUM TIMES.

Cikin Maris ne aka rika watsa wani bidiyo a soshiyal midiya, inda aka nuno Adeniyi cikin sojoji ya na korafin rashin wadatattun makamai, bayan Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya da dama a wani gumurzu da suka yi.

Adeniyi dai na cikin sojoji 886 da rundunar sojan Najeriya ta lissafa za a yi wa canjin wurin aiki a ranar Talata.

Sunan sa ne na 42. Za a maida shi Hedikwatar Sojoji ta Abuja, daga Cibiyar Bunkasa Harkokin Sojoji da ke Abuja din ita ma.

Bayani ya ce za a tura shi can “for jurisdiction”. Fassarar wannan Turanci kamar yadda majiyar PREMIUM TIMES ta bayyana, na nufin fuskantar tuhuma a asirce, ko kuma ‘court-martial’.

A cikin bidiyon da ya janyo wa Manjo Janar Adeniyi shiga tsomomuwa, an nuno shi a cikin gungun sojojin da ke cikin matukar damuwa, ya na korafin rashin ingantattun makamai domin fuskantar Boko Haram.

Hakan ya faru ne bayan Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya da dama a wani gumurzu da Adeniyi ya ce Boko Haram sun kewaye su day motocin yaki 15.

Ya yi korafin kuma cewa rashin samun bayanan sirri ya kawo rasa rayukan sojoji da dama a lokacin.

Sai dai kuma a cikin bidiyon ya ce shi da sauran sojojin za su ci gaba da jajircewa su fuskanci ‘yan ta’adda.

Wannan bidiyo ya haifar da fushi da fusatar ‘yan Najeriya, wadanda suka harzuka suka rika sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da shugabannin sojoji.

Yayin da mahukuntan sojoji ba su yi magana kan bidiyon va. Amma kuma nan da nan cikin gaggawa aka dauke Adeniyi daga matsayin Kwamandan ‘Operation Lafiya Dole’, zuwa Cibiyar Bincike ta NARC da ke Abuja.

Yanzu kuma za a maida shi hedikwata domin ya fuskanci tuhuma.

Masana abin da ake ciki sun ce sojoji sun bari sai da hayaniyar bidiyon ta lafa, sannan suka taso da batun tuhumar Adeniyi.

Ana tunanin zai fara bayyana a gaban kotun bincike ta sirri a ranar 20 Ga Yuli.

PREMIUM TIMES ta kasa samun Kakakin Sojoji, Sagir Musa, domin karin bayani.

Share.

game da Author