Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa, biyo bayan yanke jikin da Shugaban Hukumar NDDC ya girde ya fadi, daga yanzu ba sai ya sake halartar Zauren Zaman Kwsmitini Bincike ba.
Ya ce tunda dai ya damka wa masu bincike dukkan kwafe-kwafen takardun bayanan yadda aka kashe kudaden, ya je ya ci gaba da jiyyar daukewar nunfashin da ya sa shi yanke jiki ya fadi a Majalisa.
Pondei ya fadi na a Zauren Sauraren Binciken Badakalar Kashe Naira Bilyan 40 na Hukumar Bunkasa Yankin Neja-Delta.
Gbajabiamila ya bai wa Pondei hakurin sarkewar numfashin da ya yi sanadiyyar rashin wadataccen iska a zauren bincike.
Daga nan kuma ya yi masa fatan samun sauki da murmurewa cikin gaggawa.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Shugaban NDDC ya yanke jiki ya fadi, yayin da Kwamitin Bincike ke sheka masa ruwan tambayoyi.
Rincimi ya barke a Zauren Sauraron Zaman Kwamitin Binciken Harkallar Hukumar NDDC a Majalisar Tarayya, daidai lokacin da Shugaban Riko na hukumar ya yanke jiki ya zube kasa, lokacin da ya ke amsa ruwan tambayiyin da kwamitin bincike ke shekara masa a ranar Litinin din nan.
Daniel Pondei ya zube kasa, hakan kuma ya kawo karshen zaman, inda aka garzaya da shi asibiti. Ita kuma Majalisa ta bayar da hutun mintina 30.
Ya bayyana ne a Majalisa domin ci gaba da amsa tambayoyi, bayan ya fusata a ranar Alhamis ya fice daga Zauren Majalisa, kuma ya zargi Shugaban Kwamitin Bincike Olubunmi Tunji-Ojo da karbar rashawar kwangila a NNDC.
A zaman na ranar Litinin, Tunji-Ojo ya sauka daga shugabancin Kwamitin Bincike ba da wata-wata ba, saboda zargin da Pondei ya yi masa.
An maye gurbin sa da mataimaki, wato Thomas Ereyifomi.
An dai shirya yi wa Pondei da Ministan Neja-Delta, Godswill Akpabio tambayoyi a yau.
Bayan kowa ya hallara, har da Akpabio da ya isa 11:23 na rana, an fara zaman kwamiti ta hanyar rantsar da Pondei cewa zai bayyana gaskiya.
Daga nan aka sallami jami’an tsaro aka ce su fice daga zauren.
Pondei ya rika bayanin yadda Hukumar NDDC ta kashe naira bilyan 81.5 dalla-dalla, ya na mai cewa, wadannan kudade NDDC ta karbe su ne daga Gwamnatin Tarayya, tsakanin Oktoba zuwa Mayu, 2019.
Sannan kuma ta karbi bilyan 34 tsakanin Janairu zuwa Mayu, 2020.
Ya ce NDDC ta kashe naira bilyan 51.9 wajen hidimomi daban-daban.
Ta kuma kashe naira bilyan 38.6 wajen gudanar da manyan ayyukan Hukumar a yankunan Neja-Delta.
Ya ce dukkan wani otal-otal da ke Fatakwal ya na bin NDDC bashi tsawon shekaru uku, tun cikin 2016, amma zuwan shi Pondei NDDC duk ya biya su kudaden su.
Akwai kudin alawus na ayyukan ma’aikata da ya ce kuma ya biya kowane naira 500,000. Ya ce shekaru uku ba a bai wa kowa ko sisi ba, sai hawan sa shugabancin hukumar.
Sai kuma wani titi a Fatakwal mai suna ‘Infant Jesus’ da ya ce an dankara makudan kudade wajen gina shi.
Sannan ya ce kudin tallafin Korona da ya ce ya biya ga su kan su, naira bilyan 1.32 ne, ba naira bilyan 1.5 ba.
Ya na cikin bayani ne sai ya yanke jiki ya zube kasa.