BINCIKEN MAGU: ‘Yan Najeriya za su sha mamakin fallasar da za a bankado -Fadar Shugaban Kasa

0

Fadar Shugaba Muhammadu Buhari ta bayyana cewa ‘yan Najeriya su yi zaman jiran gani da al’ajabin irin abin da Kwamirin Binciken Magu zai fallasa, bayan kammala binciken sa.

Kakakin Yada Labarai na Shugaban Kasa, Garba Shehu ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da yi da Gudan Talbijin na Channels, ranar Lahadi.

Shehu ya ce wannan bincike da ake kan gudanarwa ya kara nuna cewa Shugaba Buhari mutum ne mai kyamar rashawa da cin hanci, kuma bai yarda da tafiya a kan haka ba.

Ya ce Kwamitin Bincike karkashin Tsohon Cif Jojin Najeriya, Ayo Salami kan sanar da Buhari abin da suka bankado akai-akai.

Saboda haka ya ce jama’a su rika yin nesa-nesa da wasu rahotannin da ake bugawa masu muzanta kokarin da Kwamitin Bincike ke yi.

An fara binciken Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu, bayan an kama shi an tsare, bisa wasu zarge-zargen da Ministan Harkokin Shari’a, Abubakar Malami ya yi masa na yi wa kudaden da ya kwato abin nan da Hausawa ke kira sata-ta-saci-sata.

Shehu ya ce nan ba da dadewa ba Kwamitin Bincike zai bayyana rahoton sa a fili.

Share.

game da Author