A cigaba da binciken shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu da kwamitin shugaban kasa ke yi, ranar Laraba kuma aka sanar da dakatar da sakataren hukumar kuma shugaban ma’aikatan hukumar Olanipekun Olukoyede da wasu manyan darektocin hukumar.
Baya ga su dakatarwar ya hada wasu daga cikin shugabannin hukumar na shiyya.
Akalla manyan darektoci 11 ne wannan dakatarwa ya shafa duk da cewa ba a aiko musu da takardar dakatarwar ba tukunna.
Wani daga cikin darektocin da aka gayyata domin bayyana a gaban kwamitin ya ce ” mambobin kwamitin sun umarce mu da mu mika musu duka takardun bincike na hukumar, amma sai muka gaya musu cewa hakan ba zai yiwu ba.
” Daga nan ne fa muka gano cewa wannan bincike, bita da kulli ne amma sam ba wai don Magu ya aikata laifi ba, akwai kullalliya a kasa da ake shiryawa.”
Dakataccen shugaban riko na hukumar EFCC Ibrahim Magu na tsare a hukumar ‘Yan sanda inda ake tuhumarsa da zargin yin harkallar wasu kadarori da dukiyar hukumar bayan ya kwato su daga barayin gwamnati.
Magu ya karyata duka zargin da kwamitin ta yi masa.
A cigaba da zaman kwamitin ranar Laraba kuma sai aka sanar da dakatar da sakataren hukumar EFCC din da wasu manyan darektocin hukumar.
Daya daga cikin harkallar da ake tuhumar Magu akai shine wai ya waske da ribar wasu kudade da aka ajiye na hukumar a banki.
Bayan bincike an gano babu wani abu mai kama da haka da ya auku, hatta a gaban kwamitin da ke bincikar Magu.