Sakamakon binciken kwakwaf da wakilin PREMIUM TIMES yayi kan yadda marasa lafiya ke fama da rashin kula da ake musu a wasu asibitocin dake babban birnin tarayyar Najeriya, yayi matukar munin da ya kai ga sai mara lafiya ya bada cin hanci kafin likita ya duba shi.
Marasa lafiya kan bada cin hanci domin ganin likita,domin samun katin ganin likita, gadon kwantar da mara lafiya, magungunan da ake bada su kyauta da sauran su.
Sai dai kuma duk da wadannan korafe-korafe da aka jiyo daga bakin wasu marasa lafiya, likitocin wasu asibitocin sun karyata hakan.
Bincike
An gudanar da wannan bincike a wasu zababbun asibitocin gwamnati dake Abuja sannan akan mutum 300 da ke yawan zuwa wasu daga cikin asibitocin gwamnati da ka Abuja.
Da yawa daga cikin mutanen da suka tattauna da wakilin PREMIUM TIMES sun shaida cewa a ko da yaushe suka garzaya asibiti domin ganin likita don wani ciwo da ayake damun su, sukan karae ne dai sai sun rika bada yan kudade na cin hanci domin su samu damar ganin likita ko kuma a duba su yadda ya kamata.
Akalla mutum 134 sun tabbatar cewa sukan biya kudi domin samun damar ganin likita. Wasu kan bada naira 200 wasu kuma har 21,000 domin kawai su samu likita ya duba su.
Likitoci basu karbar cin hanci
Shugaban asibitin ‘Clinical and Diagnostic Services’ Francis Alu ya karyata korafin wadannan marasa lafiya da suke cewa wai sai sun biya cin hanci kafin likita ya duba su.
Shugaban kungiyar likitoci ARD Roland Aigbovo ya ce lalllai akwai yiwuwar ana samun wadanda suke yin haka amma kuma ba kamar yadda ake yayadawa ba.
“A asibitocin gwamnati dake nan Abuja an lika har a bango domin kowa ya gani cewa duk kudaden da mutum zai biya a asibiti ya biya a wurin da ake biyan kudi sannan mutum ya karbi risit.
Idan mara lafiya ya biya ma’aikacin kiwon lafiya kudi wannan tsakanin sa ne da ma’aikacin kiwon lafiya.
Aigbovo ya ce mafi yawan asibitocin gwamnatin dake Abuja na fama da karancin gadajen kwantar da marasa lafiya wanda haka ke hana mutane samun kulan da ya kamata musamman wadanda ke bukatan Kula cikin gaggawa.
Aigbovo ya Kuma kwabi yadda wasu ma’aikatan asibiti ke karban kudi kafin su ciro Katin Mara lafiya.
Bayan haka Shugaban ‘Tap Initiative’ Martins Obono bai amince da abin da ma’aikatan kiwon lafiyan suka fada ba.
Aigbovo ya kara da cewa ma’aikatar kiwon lafiya da hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya ta kasa NHPCDA su yi amfani da sakamakon wannan bincike domin hukunta ma’aikatan kiwon lafiyan dake karban cin hanci a asibitocin gwamnati.
Wani likita mai suna Abiodun Essiet ya yi Kira da a Kara yin da bincike kan sakamakon wannan bincike domin tsara hanyoyin kawar da matsalar karbar cin hanci a asibitocin Abuja.
Discussion about this post