Ministan Harkokin Sufuri Rotimi Amaechi ys bayyana cewa binciken tulin basukan da Gwamnatin Tarayya ta ciwo, wanda ake yi a Majalisar Tarayya, zai iya jefa shakku ga kasashen waje su daina bai wa kasar nan basukan da suka yi alkawarin kara narka mata.
Amaechi ya yi wannan furucin a gaban mambobin Kwamitin Duba Yarjejeniya tsakanin gwamnati da wasu da wasu kamfanonin bayar da ramce ko zuba a jari da kuma gudanar da ayyukan kwangiloli.
Ministan ya ce shi dai ya na goyon bayan a dage binciken da ake yi, domin idan aka ci gaba fa to manyan masana’antun zuba jari za su yi fargabar sakar wa Najeriya dimbin basukan da za su bayar nan ba da dadewa ba.
Ya kara da cewa aikin karasa titin jirgin kasa daga Lagos zuwa Ibadan har Kano zai samu cikas idan aka hana Najeriya wannan bashi.
Sai ya ce ya bai wa Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila shawara a dage zaman binciken sai cikin Disamba, bayan Najeriy ta karbo basukan, sai a ci gaba da tonon sililin da za a ci gaba da yi.
Baya gs wannan Kwamitin Bincike, cikin makon jiya ne aka kammala zaman Kwamitin Binciken Hukumar Bunkasa Neja-Data.
Sannan kuma ranar Alhamis aka kafa wani kwamiti da zai binciki yadda aka ragargaje naira bilyan 100 cikin shekara daya a Hukumar Farfado Da Yankin Arewa maso Gabas.